Sanatocin PDP Sun Gindaya Sharaɗin Shiga Haɗakar Su Atiku domin Kifar da Tinubu a 2027

Sanatocin PDP Sun Gindaya Sharaɗin Shiga Haɗakar Su Atiku domin Kifar da Tinubu a 2027

  • Sanatocin PDP a Majalisar Dattawa ta 10 sun ce ba su adawa da yunƙurin kafa haɗaka da nufin kifar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • A wani taro da suka yi ranar Talata, sanatocin PDP sun kafa sharaɗin da zai sa su haɗe da masu shirin haɗakar ƴan adawa a Najeriya
  • Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ya ce har yanzu PDP na nan da ranta kuma za ta dawo kan ganiyarta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanatocin jam’iyyar PDP a Majalisar Dattawa sun bayyana cewa ba su adawa da kokarin kafa haɗakar jam’iyyun siyasa don hambarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Sai dai sanatocin sun bayyana cewa za su shiga haɗakar ne kawai idan ta kasance za a ƙulla ta karkashin jagorancin jam’iyyu, ba wasu ɗaiɗaikun mutane ba.

Sanata Abba Moro.
Yan PDP a Majalisar Dattawa suk bayyana matsaya kan shirin kafa haɗaka domin kayar da Bola Tinubu a 2027 Hoto: Comrade Abba Moro
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro (Benue ta Kudu), ne ya sanar da hakan bayan wata ganawa da suka yi a Abuja ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane sharadi sanatocin PDP suka gindaya?

Ya ce duk wani ƙawance da za a ƙulla a siyasa, kamata ya yi a ce jam'iyyu ne suke jagoranta ba wasu tsirarun mutane ba matukar ana son samun nasara.

“Sanatocin PDP ba sa adawa da ra’ayin kafa haɗaka. Amma muna ba da shawarar cewa kowanne irin haɗaka za a yi ya kamata jam’iyyun siyasa su jagoranta, ba ɗaiɗaikun mutane ba.”
"A matsayin babbar jam’iyyar adawa, PDP tana da wadaccen wurin da za ta ɗauki dukkan masu sha’awar kafa irin wannan haɗaka. Don haka, idan haɗakar ta zama dole, PDP ya kamata ta jagorance shi.”

- Sanata Abba Moro.

Yadda Atiku, Obi da El-Rufai suka faro shirin haɗaka

Idan ba ku manta ba a ranar 20 ga Maris, manyan jagororin adawa suka sanar da shirinsu na kafa haɗaka domin daƙile burin shugaban kasa, Bola Tinubu na tazarce a 2027.

Waɗanda su ka sanar da haɗakar sune ɗan takarar shugaban kasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar; takwaransa na LP, Peter Obi; da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Jawabin Sanata Moro ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Atiku na duba yiwuwar tsayawa takara karkashin wata jam’iyya daban.

Haka kuma, ana rade-radin cewa shi da Peter Obi sun amince su yi aiki tare karkashin tutar jam’iyyar ADC, kamar yadda The Nation ta kawo.

Damagum.
Sanatocin PDP sun sha alwashin dawo da jam'iyyar kan ganiyarta Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam'iyyar PDP ta kama hanyar rushewa?

Har ila yau, Sanatocin PDP sun kuma karyata rade-radin da ke cewa jam’iyyar ta kama hanyar rugujewa, inda suka jaddada cewa har yanzu PDP tana da karfi.

“Rigimar da PDP ke ciki a yanzu ba sabuwa ba ce. Sauran jam’iyyun adawa har ma da jam’iyyar APC mai mulki suna fuskantar irin wannan rikici a cikin gida," in ji Abba Moro.

Ya bukaci duka ƴan PDP da su ci gaba da kasancewa masu gaskiya, biyayya da jajircewa, tare da nuna kwarin gwiwar cewa PDP za ta dawo kan ganiyarta.

PDP ta yi hasashen nasarar haɗaka a 2027

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta bayyana cewa kawancen, Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai na iya kawo ƙarshen mulkin APC a 2027.

Sai dai PDP ta ce nasarar hadakar ta dogara ne kan kyaun niyya, hadin kai da kuma iya amfani da fushin jama’a duba da halin ƙuncin rayuwa da suke ciki.

Mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa, Hon. Timothy Osadolor, shi ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262