2027: Shugaba Tinubu Ya Kara Karfi, Ya Samu Goyon Bayan Gwamnonin Jam'iyyun Adawa 3

2027: Shugaba Tinubu Ya Kara Karfi, Ya Samu Goyon Bayan Gwamnonin Jam'iyyun Adawa 3

  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ya ce gaba ɗaya gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas suna goyon bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya ce gwamnonin sun jingine batun banbancin siyasa, sun koma bayan Tinubu
  • Ya ce dama koken ƴan kabilar Ibo ba ya wuce rashin ayyukan raya ƙasa wanda kuma a yanzu gwamnatin Bola Tinubu na yi wa yankin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi - Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya ce dukkan gwamnonin yankin Kudu Maso Gabas suna goyon byan tazarcen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Umahi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wani shirin bidiyo da za a saki a bikin cikar gwamnatin Shugaba Tinubu shekaru biyu a mulki.

David Umahi.
Gwamnoni Kudu maso Gabas na tare da Bola Tinubu, in ji Umahi Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Babban mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Kudu maso Gabas na tare da Tinubu

Ministan ya ce duk da banbancin jam’iyyun siyasa, gwamnonin Kudu Maso Gabas suna goyon bayan gwamnatin Tinubu, saboda yadda take nuna kulawa da yankin wajen aiwatar da manyan ayyukan raya kasa.

“Mutumin Ibo yana da kwazo, kuma Allah ya ba shi hikima. Abin da 'yan yankin Kudu Maso Gabas ke nema shi ne adalci da daidaito, kuma hakan ne Shugaba Tinubu ke kokarin yi yanzu.
"A da, a matsayina na gwamna ko mataimaki, babban korafinmu a Ebonyi shi ne rashin ayyukan gwamnatin tarayya. Amma a yau, ba ma jin wannan koke-koken.”

- Dave Umahi.

Ayyukan da Tinubu ke yi a Kudu maso Gabas

Umahi ya jaddada cewa akwai ayyukan tituna da dama da ake aiwatarwa a yankin, ciki har da titin Fatakwal zuwa Enugu, Enugu zuwa Abakaliki, Enugu zuwa Onitsha da titin Onitsha zuwa Owerri

Sai kuma gadar Neja wacce ministan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta biya kashi 30 cikin 100 na kudin aikin.

Umahi ya kuma bayyana cewa an kusa kammala wani bangare na titin gabar tekun Lagos zuwa Kalaba kuma daga watan Disamba za a fara karbar kudin haraji daga masu amfani da titin.

Dave Umahi.
Shugaba Tinubu ya kara samun goyon baya daga gwamnonin Kudu maso Gabas Hoto: Dave Umahi
Asali: Twitter

Gwamnonin adawa 3 da suka goyi bayan Tinubu

Gwamnonin da ke mulki a jihohin Kudo maso Gabas sun haɗa da, Alex Otti (Abia), Farfesa Chukwuma Soludo (Anambra), Francis Nwifuru (Ebonyi), Dr Peter Mbah (Enugu) da Hope Uzodimma (Imo).

Daga cikinsu APC na da guda biyu, Gwamna Uzodima na Imo da Gwamna Nwifuru na Ebonyi, yayin da PDP ke da gwamna ɗaya watau Peter Mbah na Enugu.

Sai kuma jam'iyyar APGA da ke da gwamna guda ɗaya, Charles Soludo na Anambra da kuma LP wacce ke mulki a jihar Abia karkashin Gwamna Alex Otti.

Umahi ya ce duka waɗannan gwamnonin sun amince za su ci gaba da marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

PDP ta reshen Kudu maso Gabas ta yi barazana

A wani labarin, kun ji cewa shugabannin PDP a Kudu maso Gabas sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar idan ba a naɗa Sunday Udeh-Okoye a matsayin Sakatare ba.

Kungiyar jagororin PDP na yankin ta tunatar da cewa tun bara suka amince da Udeh-Okoye ya rike mukamin, amma aka yi watsi da bukatarsu.

Shugabannin sun gargaɗi PDP cewa wannan lamarin ba abin da za a yi wasa da shi ba ne domin zai iya jawo gagarumar matsala ga babbar jam'iyyar adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262