Uba Sani Ya Kalubalanci El Rufai da Sauran Masu Shirin Kawar da Tinubu a 2027
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya taɓo batun shirin wasu ƴan siyasa na kawar da Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027
- Uba Sani ya nuna takaicinsa kan yadda wasu daga cikinsu suka riƙa yin kalamai waɗanda za su iya tunzura al'umma
- Gwamnan ya ƙalubalanci ƴan siyasan da su fito su gwada farin jininsu a zaɓen 2027, su gani ko za su iya kai labari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ƙalubalanci Nasir El-Rufai da sauran ƴan siyasan da ke shirin yin haɗaka domin kawar da Bola Tinubu a 2027.
Gwamna Uba Sani ya ƙalubalanci ƴan siyasan da suke ganin za su iya karawa da shugaban ƙasan, da su fito su gwada farin jininsu a zaɓen 2027 mai zuwa.

Asali: Twitter
Gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar TVC News a ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uba Sani ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu daga cikin waɗanda aka kafa jam’iyyar APC da su, suke sukar mulkin shugaba Tinubu.
El-Rufai da Amaechi sun caccaki Tinubu
A cikin ƴan kwanakin nan dai, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun caccaki gwamnatin Tinubu a taron tattaunawa kan inganta dimokuradiyya a Najeriya.
El-Rufai ya ce APC ta yi watsi da manufofinta na asali kuma tana tafiyar da mulki mara inganci.
Daga baya ya bayyana cewa zai ci gaba da sukar jam'iyyar APC, ko da kuwa yana cikin gwamnatin Tinubu.
A nasa ɓangaren, Amaechi ya ce Tinubu da ƴan siyasa ba za su miƙa mulki ga matasa ba sai an kai ruwa rana.
Me Uba Sani ya ce kan shirin kawar da Tinubu?
"A matsayina na mamba a jam’iyyar APC, muna tattaunawa da juna. Ba zan ce ba mu yin kuskure ba, amma mafi yawan waɗanda ke sukar mulkin Tinubu suma ƴan jam’iyyarmu ne."
"Yawancinsu suna daga cikin waɗanda aka kafa APC da su ne. Shi ya sa na yi matuƙar mamaki lokacin da na ji wata gamayyar ƴan siyasa na haɗuwa a irin wannan lokacin suna yin waɗancan maganganun."
"Abin takaici ne, domin wasu daga cikinsu har suna kiran jama’a su ɗauki doka a hannunsu da kuma nuna adawa da gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba a dimokuradiyya."
"Ina so in fayyace cewa muna cikin dimokuraɗiyya, kuma akwai kusan shekaru biyu da rabi kacal zuwa zaɓe na gaba."
"Duk wani ɗan siyasa da ke tunanin yana da farin jini ko zai iya kayar da Bola Ahmed Tinubu ko jam’iyyar APC, kamata ya yi ya je ya yi aiki tuƙuru domin ya tsaya takara a 2027."
"Har yanzu akwai lokaci. Za su iya komawa su shirya tare da tara magoya bayansu. Amma a matsayina na gwamna, zan iya cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana aiki sosai kuma ta samu nasarori masu yawa.”

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya tuna da iyalan babban jami'in sojan da 'yan Boko Haram suka kashe
- Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya faɗi alaƙarsa da El-Rufai
A wani labarin kuma kun ji cewa gwamnan jihar Ƙaduna, Uba Sani, ya yi magana kan alaƙar da ke tsakaninsa da magabacinsa, Nasir Ahmad El-Rufai.
Uba Sani ya bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da El-Rufai wanda ya bayyana a matsayin abokinsa kuma ɗan uwa.
Gwamna Uba Sani ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan cewa gwamnatinsa na yi wa tsohon gwamnan na Kaduna bi-ta-da-ƙulli.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng