Hadimin Ganduje Ya Fadi Zabi 3 da Suka Rage wa Kwankwaso a Siyasa
- Hadimin Shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso na da zaɓi uku kafin zabe ma zuwa
- Ya bayyana cewa jagoran Kwankwasiyya na da damar yin tunani kan ko zai sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ko hadakar su Atiku Abubakar
- Amma a cewar Salihu, Kwankwaso zai iya shiga APC ne kawai a ƙarƙashin babban abokin hamayyarsa, Abdullahi Umar Ganduje
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hadimin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya ce zabi uku ya rage ga jagoran NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Salihu Yakasai ya bayyana ra'ayinsa kan mafitar da ta rage wa tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso a lokacin da masoyan Ganduje ke fatan dakile shigarsa APC.

Asali: Facebook
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Yakasai ya zayyana dabaru uku da ya ce su ne zaɓuɓɓukan da Kwankwaso ke da su kafin babban zaɓen 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon hadimin Ganduje ga Kwankwaso
Salihu Tanko Yakasai ya ce daya daga cikin zaɓuɓɓukan da Kwankwaso ke da su shi ne shiga jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Ya bayyana cewa Kwankwaso na da damar shiga APC idan aka amince da hakan bisa wasu sharadin zama a karkashin Ganduje.

Asali: Facebook
Haka kuma, a cewarsa, yana da zaɓin haɗa kai da Atiku Abubakar a hadakar adawa da aka kafa ko kuma ya ci gaba da zama a NNPP.
A wani yanayi na cin mutunci, Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu a dandalin X, ya kira NNPP mai mulkin jihar Kano da kayan gwari.
Ya ce:
“Ko ka shigo APC ƙarƙashin Ganduje, ko ka shiga haɗakar adawa ƙarƙashin Atiku, ko ka zauna a kayan gwari a NNPP, shawara ta rage wa Jagora.”
Masoya Kwankwaso sun soki hadimin Ganduje
Sakon da Yakasai ya wallafa bai yi wa magoya bayan Kwankwaso daɗi ba, inda da dama suka caccake shi da sukar yadda ya zama daga tsohon dan takarar gwamna zuwa yaron Ganduje.
Abubakar Ibrahim ya rubuta:
"Wallahi kai ka san ko yau ya shigo, to fa, bacci babu a wannan dare. Sai kun fara taruka, ta ina za a fara? "
Ibrahim Hamza ya ce:
"A cikin kayan gwarin ya kore ku daga Kano. Korar da ba za ku dawo ba, in sha Allah."
Khalifa Idris ya wallafa cewa:
"Dan takarar gwamna na farko da ya koma ɗan soshiyal midiya. Allah kare mu da ƙarshen siyasa irin ta Salihu Tanko Yakasai."
Mansur Khalid Idris ya ce:
"Na yi mamaki da jin cewa a ƙarshen maganarka ka kira Kwankwaso da ‘Jagora’. Lallai, ko kura ta mutu, kura ce. RMK 2027 in sha Allah."
Tafiyar Kwankwaso ta samu tagomashi a Kano
A baya, kun ji cewa Rabi'u Musa Kwankwaso, ya karɓi tsofaffin jami’an soja 24 da suka yi ritaya daga rundunar sojojin Najeriya, wadanda suka nuna goyon baya ga Kwankwasiyya.
Duka tsofaffin jami'an'yan asalin jihar Kano ne, kuma sun kammala aikinsu da rundunar soji a watan Janairu 2025, bayan sun kwashe shekaru 35 suna yi wa ƙasa hidima.
Tawagar ta zo ne ƙarƙashin Kabiru Haruna Getso, shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kano, kuma sun ce su shiga Kwabkwasiyya saboda kyakkyawar manufarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng