Duk da Rigimar Kwankwaso da NNPP, Tafiyar Kwankwasiyya Ta Samu Tagomashi a Kano

Duk da Rigimar Kwankwaso da NNPP, Tafiyar Kwankwasiyya Ta Samu Tagomashi a Kano

  • Tafiyar Kwankwasiyya ta samu ƙaruwa a jihar Kano bayan wasu tsofaffin sojoji sun shigo cikinta
  • Madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya tarbi tawagar wacce ta ƙunshi mutane 24
  • Kwankwaso ya nuna farin cikinsa kan matakin da tsofaffin jami'an sojojin suka ɗauka na shigowa cikin tafiyar Kwankwasiyya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi wata tawaga da ta shigo cikin tafiyar.

Kwankwaso ya karɓi tawagar wacce ta ƙunshi manyan jami’an soja 24 da suka yi ritaya, waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga tafiyar Kwankwasiyya.

Rabiu Musa Kwankwaso
Tafiyar Kwankwasiyya ta samu karuwa a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce jami’an waɗanda dukkansu ƴan asalin jihar Kano ne, sun yi ritaya ne a watan Janairu na shekarar 2025 bayan sun yi shekaru 35 suna hidima a rundunar sojojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwasiyya ta ƙara ƙarfi a Kano

Matakin da suka ɗauka na shiga tafiyar Kwankwasiyya ya zama wata babbar alama ta karɓuwar tafiyar a matakin ƙasa, tare da ƙarfafa ƙungiyar, musamman yayin da zaɓe ke ƙaratowa.

Tawagar ta zo ƙarƙashin jagorancin Hon. Kabiru Getso Haruna, shugaban hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Kano.

Hon. Kabiru Haruna Getso ya bayyana matakin nasu a matsayin zaɓi mai kyau duba da irin hangen nesa da tafiyar Kwankwasiyya ke da shi.

Kwankwaso ya yi jawabin godiya

A lokacin da yake karɓar tawagar a birnin Kano, Kwankwaso ya nuna matuƙar godiyarsa da jin daɗinsa, inda ya yaba da irin gudunmawar da suka bayar wajen hidimatawa ƙasa.

Ya kuma tabbatar musu da cewa za su samu muhimmin matsayi a tafiyar wajen inganta dimokuraɗiyya, haɗin kai da ci gaba.

"Wannan lokaci ne na alfahari da girmamawa. Waɗannan mutanen sun yi wa ƙasa hidima cikin ƙwazo da sadaukarwa, kuma yanzu sun yanke shawarar shiga tafiyar domin ci gaba da hidima ga dimokuraɗiyya da al’umma."

"Goyon bayansu zai ƙarfafa mu sosai wajen gina Najeriya mafi inganci."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya tarbi sababbin 'yan Kwankwasiyya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso ya ƙara da cewa shigowar ƙwararru masu mutunci kamar tsofaffin jami’an soja yana da matuƙar amfani wajen gina tafiyar siyasa da ta haɗa kowa da kowa, wacce ta ginu kan ginshiƙan ƙwarewa, ɗa’a da hidima ga jama’a.

Karanta wasu labaran kan Kwankwasiyya

NNPP: Barau ya karbi matan Kwankwasiyya zuwa APC a Abuja

NNPP: Barau ya kwashe 'yan Kwankwasiyya zuwa APC a dukkan shiyyoyin Kano

Kano: Jiga jigai 4 sun rabu da Kwankwaso da NNPP, Kwankwasiyya ta yi martani

Kwankwaso ya musanta batun sauya sheƙa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan batun cewa yana shirin sauya sheƙa.

Ƙwankwaso ya ƙaryata jita-jitar wacce ke cewa ya shirya tsaf domin barin jam'iyyarsa ta NNPP.

Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya bayyana cewa ya daɗe da daina tsoma baki kan abubuwan da ke faruwa a fagen siyasar Najeriya, har sai zuwa wani lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng