Rigima ta Kunno Kai a APC ana Shirin Karɓar Sanatoci 3, an Dakatar da Manyan Jiga Jigai 10
- Rikici na neman ɓarkewa a jam'iyyar APC da aka dakatar da tsohon ɗan Majalisar Tarayya, Muhammad Shehu Koko da wasu shugabanni
- Jam'iyyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Koko da shugabannin jam'iyya guda tara na ƙaramar hukumar Koko a jihar Kebbi
- Takardar dakatarwar ta nuna cewa APC ta ɗauki wannan matakin ne bisa zarginsu da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa da rashin ladabi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi - Rikici na neman ɓarkewa a jam'iyyar APC reshen Kebbi kwanaki kalilan bayan sanatocin uki na jihar sun amince za su baro PDP zuwa APC.
Jam'iyyar APC a Kebbi ta sanar da dakatar da tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Koko/Maiyama, Hon. Muhammad Shehu Koko.

Asali: Facebook
Rahoton Vanguard ya tattaro cewa APC ta kuma dakatar da shugabanninta guda tara a ƙaramar hukumar Koko da ke jihar Kebbi a Arewa maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rigima ta kunno kai a APC ta jihar Kebbi
Ana ganin wannan lamari alamu ne na ɓarakar da ke neman kunno kai a APC reshen jihar Kebbi a lokacin da jam'iyyar ke shirin karɓar sanatoci uku daga PDP.
Sanatocin da ake sa ran za su koma jam'iyyar APC sun haɗa da Adamu Aleiro (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abubakar Abdullahi (Kebbi ta Arewa) da Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu).
Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa sanatocin sun amince za su koma APC bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja.
APC ta dakatar da shugabanni 9 a Kebbi
Kwanaki kaɗan bayan haka, APC a Kebbi ta dakatar da tsohon ɗan Majalisar Wakilan tarayya da wasu shugabanninta a ƙaramar hukumar Koko.
Daga cikin wadanda aka dakatar har da:
1. Muhammad Danyado - Mataimakin Shugaban APC na Koko.
2. Biyaminu Muhammad - Sakataren jam’iyyar
3. Talatu Zauro - Shugabar Mata
4. Maude Muhammad - Shugaban Matasa
5. Umaru Aliyu - Sakataren Kudi
6. Aminu Bacha - Sakataren Walwala da Jin Daɗi
7. Kabiru Fadi Zaria - Mataimakin Sakataren Tsare-Tsare
8. Abdullahi Ɗanyaya - Mataimakin Kakakin Jam'iyya
9. Ibrahim Ajona - Tsohon Shugaba.
Me yasa APC ta dakatar da jiga-jiganta?
A cewar takardar dakatarwar da Channels TV ta samu, matakin ya biyo bayan zarginsu da cin amanar jam’iyya, rashin biyayya, da cin zarafin shugabannin APC a yankin.
Takardar ta samu sa hannun shugaban APC na karamar hukumar Koko, Muhammad Maibarga, ciyaman na Koko, Sirajo Usman Koko, da wasu shugabannin jam'iyya 14.

Asali: UGC
Menene dailin dakatar da Hon. Muhammad Koko?
Sai dai makusantan tsohon Ɗan Majalisar Wakilai da aka dakatar sun ki yarda su yi magana kan lamarin saboda ba su da hurumin hakan.
Duk da haka wasu daga ciki sun ce dakatar da Muhammad Shehu Koko ba zai rasa nasaba da shirinsa na neman takarar sanata ba, wanda bai yi wa ƙusoshin APC daɗi ba.
Rahoton ya nuna cewa akwai yiwuwar rikici mai zurfi a jam’iyyar APC ta jihar Kebbi idan ba a sasanta bangarorin ba.
Kasa mai jam'iyya a tunanin APC
Duk da wannan rikicin da ya taso a jam'iyyar APC, wasu jam'iyyun adawa na zarginta da kokarin mayar da Najeriya kasa mai jam'iyya guda.
Jam'iyyar PDP da sauran 'yan adawa suna ganin matakan da APC ke dauka, musamman dakatar da shugabannin jam'iyya da kuma yunkurin karɓar sanatocin daga PDP, a matsayin wani ɓangare na dabarar da zai tilasta wasu jam'iyyun su koma ƙarƙashin iko ɗaya.
A cewar 'yan adawa, wannan matakin zai ƙara jefa tsarin siyasar Najeriya cikin hadari, inda za a rasa mabuɗin damammaki ga 'yan siyasa daga jam'iyyun adawa, wanda zai iya kawo cikas ga cigaba da sauyi a cikin tsarin mulkin dimokuradiyya.
Hakan na nuni da yadda APC ke ɗaukar matakan da wasu ke ganin na son kara ƙarfafa ikon ta a cikin siyasar Najeriya, wanda zai iya haifar da rarraba ƙungiyoyin siyasa da samun gamammen iko a mulki kasar.
Wannan lamari na nuna yadda APC ke fuskantar tuhuma daga 'yan adawa na kokarin canza tsarin siyasar kasar zuwa na jam'iyya guda.
Shugaban APC ya yi maraba da sanatoci 3
A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya nuna farin cikinsa da sanatocin Kebbi uku suka amince za su shiga jam'iyya mai mulki.
Ganduje, tsohon gwamnan Kano ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a shirya karbar sababbin sanatocin bisa doka da tsari.
Ya ce wannan ya kara nuna yadda jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke ƙara karɓuwa a lungu da saƙo na ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng