An kai Gyaran Sabon Jirgin Shugaban Kasa da Bola Tinubu Ya Sayo Kasar Waje

An kai Gyaran Sabon Jirgin Shugaban Kasa da Bola Tinubu Ya Sayo Kasar Waje

  • Gwamnati ta kashe Naira biliyan 20.03 wajen kula da jiragen shugaban kasa tsakanin Yulin 2023 zuwa Disamban 2024
  • Rahotanni na nuni da cewa an tura sabon jirgin Airbus A330 da Najeriya ta saye a 2024 Afrika ta Kudu domin fenti da gyare-gyare
  • Masana sun danganta hauhawar kudin kula da jiragen ne da tsadar kayayyaki da dadewar jiragen ana aiki da su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta kashe sama da Naira biliyan 20 wajen kula da jiragen shugaban kasa daga Yulin 2023 zuwa karshen shekarar 2024.

Wannan na zuwa ne yayin da aka tura sabon jirgin shugaban kasa da aka saye a bara zuwa Afirka ta Kudu domin yin gyare-gyare da canza fasalin jikinsa.

Jirgi
Ana kai jirgin shugaban kasa gyara Afrika ta Kudu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Rahoton Punch ya nuna cewa a shekarar 2024 kadai, an kashe Naira biliyan 14.15 wajen kula da jiragen, wanda ya kai kashi 71 cikin 100 na kasafin kudin da aka ware wa jiragen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce mafi yawan kudin da aka kashe sun kasance a karkashin sashen kudin da ake ware wa harkokin kasashen waje, kamar sayen fetur da gyaran jirage a kasashen waje.

Sabon jirgi na shan gyara a Afirka ta Kudu

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun tabbatar wa manema labarai cewa an tura sabon jirgin Airbus A330 da aka saya a shekarar 2024 Afirka ta Kudu domin fenti da gyare-gyare.

Jirgin mai shekaru kusan 15 da aka saye kan Dala miliyan 100 ya zo ne domin maye gurbin Boeing 737 wanda ke fama da matsalolin gyara.

Wani jami’i ya bayyana cewa an kai sabon jirgin ne don a canza masa fasalin jiki ya dace da matsayin shugaban kasa.

Wata majiya ta ce ana kuma yin wasu muhimman sababbin gyare-gyare a ciki da wajen jirgin domin inganta lafiya da aikinsa.

Ana kashe makudan kudi kan jiragen Najeriya

Rahoton ya bayyana yadda gwamnati ke ci gaba da zuba makudan kudi a kan jiragen shugaban kasa tun daga shekarar 2017 zuwa yau.

A shekarar 2017, an ware Naira biliyan 4.37, amma zuwa 2024 an kashe Naira biliyan 20.52 – karin da ya kai kashi 370 cikin 100.

Masana a fannin sufurin jiragen sama sun alakanta karin kudin da faduwar darajar Naira, tsadar gyara da kuma tsufan jiragen.

Tinubu
An caccaki Tinubu kan kashe makudan kudi a harkokin gwamnati. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Wani masani, Olumide Ohunayo ya ce ana biyan kudin mafi yawan kayayyakin gyara da horar da ma’aikata ne da Dala, don haka hauhawar canjin kudin kasashen waje ya yi tasiri matuka.

Kungiyoyi sun soki almubazzarancin gwamnati

Shugaban cibiyar yaki da cin hanci da rashawa (CACOL), Debo Adeniran, ya soki yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da kudin al’umma.

A cewarsa, maimakon gwamnati ta rage kashe-kashe, sai ma ta rungumi salon rayuwa mai tsada a lokacin da talakawa ke fama da yunwa.

Atiku ya ragargaji gwamnatin Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa ya soki yadda Bola Tinubu ke tafiyar da mulki.

Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da kokarin toshe bakin masu caccakar yadda yake tafiyar da lamarin tattalin Najeriya.

Legit ta rahoto cewa maganar Atiku Abubakar na zuwa ne bayan kama tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Gudaji Kazaure.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng