'APC Za Ta Wargaje, Ganduje zai Koma Jam'iyyar PDP,' Sule Lamido

'APC Za Ta Wargaje, Ganduje zai Koma Jam'iyyar PDP,' Sule Lamido

  • Sule Lamido ya ce akwai alamun jam’iyyar APC za ta rabu kashi-kashi nan da ‘yan watanni kadan masu zuwa
  • Tsohon gwamnan jihar Jigawan ya bayyana cewa Abdullahi Ganduje da sauran ‘yan siyasa za su koma PDP kafin 2027
  • Sule Lamido ya ce PDP na da kwarin gwiwa da karfin kwace mulkin Najeriya a hannun APC a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya bayyana cewa akwai alamun jam’iyyar APC za ta tarwatse nan ba da dadewa ba.

Tsohon gwamnan Jigawan ya ce hakan zai sa fitattun ‘yan siyasa ciki har da Abdullahi Ganduje su koma jam’iyyar PDP.

Sule Lamido
Sule Lamido ya ce Ganduje zai koma PDP. Hoto: All Progressive Congress|Sule Lamido
Asali: Facebook

Tribune ta rahoto cewa Sule Lamido ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabin sa a wajen taron jam’iyyar PDP na jiha da aka gudanar a filin taron Aminu Kano da ke jihar Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya ce yawan bambancin ra’ayoyi tsakanin ‘yan jam’iyyar APC ne zai haddasa rabuwar kan.

A cewar Sule, dukkan wadanda suka bar PDP zuwa APC za su dawo cikin jam’iyyar kafin zaben 2027, yana mai bayyana cewa PDP na shirin tashi da karfinta don kwace mulki.

Ganduje zai koma PDP inji Sule Lamido

Sule Lamido ya nuna kwarin gwiwa cewa nan da watanni shida masu zuwa, jam’iyyar PDP za ta samu sabon karfi da dawowar fitattun ‘yan siyasa da suka bar jam’iyyar.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje da sauransu za su dawo PDP domin APC za ta tarwatse.

Ya ce PDP ce jam’iyyar da ta fi kowa kwarewa da tarihi wajen mulki, don haka tana da karfin tsayawa takara a 2027.

Lamido ya bukaci mambobin jam’iyyar da kada su karaya da sauyin da wasu ‘yan jam’iyyar ke yi zuwa APC saboda tsoro ko matsin lamba daga gwamnati.

Sule ya zargi gwamnati da danne 'yan adawa

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya soki gwamnatin APC da cewa tana amfani da karfi wajen danne jam’iyyun adawa.

A cewarsa, irin wannan salon siyasa yana barazana ga zaman lafiya da daidaiton tsarin dimokradiyya a kasar nan.

Lamido
Tsohon gwamnan Jigawa ya bukaci 'yan PDP su kara hakuri. Hoto: Sule Lamido
Asali: Twitter

Ya kara da cewa Najeriya kasa ce mai albarka, amma rashin ingantaccen shugabanci na jefa ta cikin matsin rayuwa.

Shugaban PDP a Jigawa ya bukaci hadin kai

A nasa bangaren, sabon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Jigawa, Ibrahim Babandi Gumel, ya bukaci mambobin jam’iyyar da su hada kai.

Hon. Ibrahim Babandi Gumel ya ce hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar ne kadai zai sa su samu nasara a babban zaben 2027.

Rabiu Kwankwaso ya soki masu komawa APC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso ya soki 'yan adawa da suke komawa jam'iyyar APC.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce masu komawa APC suna daukar matakin ne saboda kwadayin abin duniya.

Kwankwaso ya kuma gargadi 'yan siyasar Kano da ke fada da tafiyar Kwankwasiyya wajen sauya sheka zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng