Takaitaccen tarihin Patience Jonathan yayin da ta cika shekara 63 da haihuwa

Takaitaccen tarihin Patience Jonathan yayin da ta cika shekara 63 da haihuwa

- A makon da ya shude Dame Patience Jonathan ta cika shekara 63 a Duniya

- Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin Mai dakin tsohon shugaban kasar

- Abin da ba a sani ba shi ne ta yi karatun boko, kuma ta kure aikin gwamnati

1. Haihuwa

An haifi Dame Fakabelema Jonathan a ranar 25 ga watan Oktoba, 1957 a garin Fatakwal, jihar Ribas. Ma’ana ta cika shekaru 63 a Duniya a karshen makon da ya wuce.

Wani abu da mutane ba su sani ba shi ne, shekarar Dame kusan daya da mai gidanta. Kma ana kiranta Faka (daga Fakabelema), ma’anar sunan shi ne ‘Mai tarin albarka’.

KU KARANTA: Mun yi kuskuren watsar da Jonathan mu kama APC - Shagari

2. Karatu

Patience Jonathan ta kammala firamare a 1976, daga nan ta tafi sakandare ta kuma lashe jarrabawar WAEC a 1980. A shekarar 1989 ta samu shaidar NCE, kafin ta tafi jami’a.

A jami’ar Fatakwal, Dame ta cigaba da karatunta a bangaren ilmin halittu, ta samu Digirin B.Ed.

3. Aiki

Dame Jonathan ta fara aiki ne a matsayin malamar makaranta a Stella Maris College, a Fatakwal. Daga nan ta shiga harkar aikin banki a 1997, kafin ta sake komawa aji.

Patience ta tafi ma’aikatar ilmi a jihar Bayelsa, har zuwa lokacin da mijinta ya hau mulki a 1999.

Wani abin mamaki shi ne a 2012 gwamnan Bayelsa Henry Seriake Dickson ya nada Patience Jonathan a matsayin sakatariyar din-din-din, duk da ta bar ofis tun 1999.

KU KARANTA: IPPIS: Zaman ASUU da Gwamnatin Buhari ya kare baram-baram

Takaitaccen tarihin Patience Jonathan yayin da ta cika shekara 63 da haihuwa
Patience Jonathan da Maigidanta Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

4. Iyali

Kamar yadda Wikipedia ya bayyana, Madam Patience Jonathan ta na da ‘ya ‘ya biyu da mai gidanta; namiji da mace: Arewera Adolphus Jonathan da Aruabi Jonathan.

5. Dukiya

Ana zargin Patience Jonathan da wawurar kudi a asusun gwamnati. Hukumar EFCC ta yi nasara a kan mai dakin tsohon shugaban a kotu, har ta karbe wasu daga cikin kudinta.

A 'yan kwanakin nan aka ji tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya tabbatar da cewa shi ne ya mallaki gidan talabijin na TVC da jaridar nan ta The Nation hari.

Tinubu ya ce dalilinsa na kyale mutane su kona TVC da The Nation shi ne gudaun zubar da jini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng