An Samu Rarrabuwar Kai a NNPP kan Ficewar Kawu Sumaila, Masoyansa Sun Ja Daga
- Magoya bayan Sanata Kawu Sumaila daga yankin Kano ta Kudu sun ki binsa zuwa jam’iyyar APC, sun zabi su ci gaba da zama a NNPP
- Kimanin mutum 200 sun je gidan Sanata Rabiu Kwankwaso domin bayyana biyayyarsu ga Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP
- Kwankwaso ya yaba da matakinsu, ya ce Kwankwasiyya na kokarin ciyar da matasa da mata gaba ta hanyar ilimi da ci gaban kai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An samu rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan Sanata Kawu Sumaila daga yankin Kano ta Kudu.
Daruruwan yan jam'iyyar NNPP suka ce za su cigaba da kasancewa a cikinta kuma ba za su bi Sanata Kawu zuwa jam’iyyar APC ba.

Asali: Twitter
Masoyan Kawu Sumaila sun bijire masa
Wadanda suka yi watsi da sauya sheka sun mamaye titin Miller inda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke zaune domin nuna biyayyarsu, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magoya bayan NNPP sun bayyana cewa matsayinsu na cigaba da kasancewa a NNPP ya samo asali ne bisa ka’ida, sun dage cewa Sanata Sumaila ne kadai ya sauya sheka zuwa APC.
Wadanda suka dawo jam’iyyar sun kai kimanin mutum 200, karkashin jagorancin Muntari Ibrahim Faruruwa da wasu.
Yankunan da masoyan Kawu Sumaila suka fito
Mafi yawansu sun fito daga Takai da wasu sassa na Karamar Hukumar Sumaila, inda suka sha alwashin ci gaba da goyon bayan jam’iyyar da shugabanninta.
Sun sake jaddada goyon bayansu ga akidun tafiyar Kwankwasiyya, inda suka ce:
“Mu ba ba ‘Yes Sir’ ba ne, mun zo nan ne don sanar da ku cewa mun ki zuwa APC tare da Sanata mai wakiltar yankinmu, maimakon haka, mun yanke shawarar dawowa gida.
“Muna ganin dawowa gida shi ne mafi alheri domin mu ci gaba da yada akidun tafiyar Kwankwasiyya da NNPP, da kuma ba da gudummawarmu wajen cigaban jiharmu.
“Muna fatan za a karbe mu a matsayin cikakkun mambobi tare da samun dukkan ‘yancin da sauran ‘ya’yan tafiyar ke da su.”

Asali: Facebook
Kwankwaso ya karbi masoyan Kawu Sumaila
Yayin da yake karbar wadanda suka dawo, Sanata Rabiu Kwankwaso ya tarbe su hannu bibbiyu tare da yaba da matakin da suka dauka, cewar Daily Post.
Kwankwaso ya ce:
“Ni da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, gwamnatin jihar, jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya, muna taya ku murna da wannan muhimmiyar shawara da kuka yanke."
Ya kara da cewa tafiyar Kwankwasiyya tana da manufa ta tallafa wa mutane musamman matasa da mata ta hanyar ilimi da wasu shirye-shiryen ci gaban kai da dogaro da kai.
“Ina addu’ar sauran mambobin da suka bar mu su ma su dawo gida domin ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban tafiyar da kuma jiharmu mai albarka ta Kano."
- Cewar Kwankwaso
Kwankwaso ya soki yan majalisu da suka koma APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya soki masu yunkurin fada da Kwankwasiyya a siyasa.
Sanata Kwankwaso ya ce yin hakan tamkar fada da bango ne da ba zai motsa ba suna da irin gudummawar da jam'iyyar NNPP ta ba su.
Tsohon gwamnan ya zargi wadanda suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC da cewa kudi ne da kwadayi suka rinjaye su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng