"Ba Ni da Niyyar Cutar da Kowa," Tinubu Ya Tunawa Ƴan Najeriya Dalilin Jefa Su a Walaha

"Ba Ni da Niyyar Cutar da Kowa," Tinubu Ya Tunawa Ƴan Najeriya Dalilin Jefa Su a Walaha

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba shi da niyyar jefa ƴan Najeriya cikin wahala da matakai masu tsauri da ya ɗauka
  • Mai girma Bola Tinubu ya ce ya ɗauki matakan ne domin Najeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa kuma tattalin arziki ya bunkasa
  • Tinubu ya yi ikirarin cewa duk da wahalar da ake ciki yanzu ƴan Najeriya sun fara ganin haske daga tsare-tsaren da ya ɓullo da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake kare matakan gyaran tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka bayan ya karɓi mulki a watan Mayun 2023.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ya ɗauki waɗannan matakai ne domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a ƙasar nan ba don jefa mutane cikin ƙuncin rayuwa ba.

Shugaba Tinubu da tawagar Qatar.
Shugaba Tinubu ya sake kare matakan da ya ɗauka masu tsauri Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙuncin wakili daga Sarkin Qatar, Dr Mohammed bin Abdulaziz Al-Khulaifi, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Me yasa Tinubu ke ɗaukar matakai masu tsauri?

Shugaba Tinubu ya ce sauya fasalin haraji na daga cikin muhimman matakai da yake ɗauka don sauƙaƙa kasuwanci ga masu zuba jari daga ƙasashen ƙetare.

“Muna yin gyare-gyare a tsarin haraji tare da la’akari da abin da ya faru a baya da kuma bukatar shiga zamani, matakan da muke ɗauka sun kasance masu tsauri.
"Na ɗauki matakai masu wahala domin samun ci gaba. A hankali muna ganin haske a ƙarshe,” in ji shi.

Za a karfafa dangantar Najeriya da Qatar

Shugaban ya ƙara da cewa Qatar ta samu nasarori a fannin tattalin arzikin zamani, amma lokaci ya yi da za ta taimaka wa Najeriya musamman a ɓangaren yaki da talauci, samar da abinci da jin daɗin jama’a.

Tinubu ya bayyana aniyar Najeriya na ƙarfafa dangantakar da ta faro tun bayan ziyarar da ya kai Qatar a 2024.

Tinubu da tawagar Qatar.
Najeriya za ta karfafa dangantaka da Qatar Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Ya umurci ministan tsare-tsaren kasa da kasafin kuɗi, Sanata Atiku Bagudu, ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da Qatar.

"Muna godiya da yadda muke tafiya tare a matsayin abokai. Ina murna da yadda Amir na Qatar ke ci gaba da tunawa da abubuwan da muka tattauna lokacin ziyara ta a bara."

- Bola Tinubu.

Shin manufofin Bola Tinubu na aiki?

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya tattalin arzikin kasa na kan hanyar farfaɗowa.

Shugaban wanda ya amince da wahalar da mutane ke ciki, ya ce gwamnatinsa za ta ƙara bullo da tsare-tsare masu kyau domin buyan buƙatun talakawa.

Tinubu ya ce zai ci gaba da bayyana sauye-sauyen tattalin arziki da alfanunsa ga al’ummar kasar, inda ya ce a shirye yake ya tattauna da kowa kan lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262