"Muna da Al'adu da Addini," Gwamnatin Abba Ta Haramta Wasu Shirye Shirye a Kano

"Muna da Al'adu da Addini," Gwamnatin Abba Ta Haramta Wasu Shirye Shirye a Kano

  • Gwamnatin Kano ta haramta gudanar da duk wasu shirye-shiryen siyasa na kai tsaye a gidajen radiyo da sauran kafafen watsa labarai a jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya sanar da haka a taronsa da shugabannin kafafen watsa labarai
  • Gwamanatin Abba Gida Gida ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin kawo ƙarshen ɓatanci, da tabbatar da kare al'adu da addini a jihar Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta duk wasu shirye-shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai baki daya.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki a matsayin wata sabuwar hanya da za ta dakile yaduwar kalaman batanci da kuma kare dabi’u, al’adu da tarbiyyar addini a Kano.

Gwamna Abba.
Gwamnatin Kano ta haramta shirye-shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Twitter

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa shugabannin kafafen yada labarai, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan harkoki na musamman na ma'aikatar yaɗa labarai, Sani Abba Yola ya fitar bayan wannan taro.

Me yasa Gwamnatin Abba ta hana shirye-shiryen?

Gwamnati ta ce haramcin ba don tauye ‘yancin ‘yan adawa ba ne, sai dai don kare mutuncin al’adun Kano da dabi’un addininta.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa daga yanzu duk wani bako da zai halarci shiri a kafafen yada labarai, dole ne ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da ke hana furta kalaman batanci, zagi ko cin mutuncin al’umma da addini.

Haka zalika, an gargaɗi masu gabatar da shirye-shirye da su guji tambayoyi ko motsin jiki da ka iya janyo martani mai zafi daga baƙi.

Waiya ya yaba wa kafafen watsa labarai bisa haɗin kai da suka bayar zuwa yanzu, yana mai cewa an samu raguwar kalaman rashin da’a tun bayan fara wayar da kai da gwamnati ke yi.

Gwamna Abba.
Gwamnatin Kano ta ɗauko hanyar tsftace kalamai a shiryen gidajen radiyo da talabijin Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin Kano za ta ci gaba da wayar da kai

Kazalika, ya jaddada aniyar ci gaba da wayar da kan da gwamnati ke yi wa masu gabatar shirye-shiryen siyasa, masu sharhi a kafafen yada labarai da malamai.

Kwamishinan ya ce hakan zai taimaka wajen inganta harshen muhawara da martaba da’a a fagen siyasa da hulɗar jama’a, Channels tv ta ruwaito.

A ƙarshe, shugabannin kafafen yada labarai sun sha alwashin ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sun kuma yi alkawarin gabatar da shawarwari ga gwamnati idan bukatar hakan ta taso don inganta ka’idojin watsa shirye-shirye da tabbatar da ɗa'a mu’amala.

Wani ɗan Kwankwasiyya, Malam Sa'idu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan mataki ne mai kyau idan ka duba cin mutuncin da ake a gidajen radiyo.

Ya ce da yawan mutane sun ji daɗin abin da gwamna ya yi amma ƴan adawa sun fara surutun cewa ana ƙoƙarin take masu haƙƙin faɗar albarkacin bakinsu ne.

A kalamansa ya ce:

"Cin mutunci da zagin da sojojin gona ke yi a radiyo ya yi yawa a Kano, ya kamata a taka masu birki kuma Alhamdulillah mai girma gwamna ya waiwayi lamarin, Allah Ya sa mu gane.

Gwamnatin Abba ta sake sukar Ganduje

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ƙara kokawa kan matsalolin da ta gada daga Abdullahi Ganduje a fannoni daban-daban.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta gaji tashoshin samar da ruwa da suka lalace waɗanda aka ɓarnata na miliyoyin Naira a gwamnatin da ta shuɗe.

Daga cikin wuraren da ake zargin Gwamnatin Ganduje ta lalata har da tashar samar da ruwa ta farko da aka gina a Kano tun shekarar 1930.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262