Gwamnatin Kano Ta Gano Tushen Matsalar Karancin Ruwa, Ta Nuna Yatsa ga Ganduje
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nuna takaici kan yadda aka ɓarnata tashoshin samar da ruwan sha a Kano a shekarun baya
- Kwamishinan ruwa na jihar Kano ya ce an lalata wuraren samar da ruwan ne a ƙarƙashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje
- Hon. Umar Doguwa ya nuna cewa sai gwamnati ta kashe miliyoyin daloli idan tana son wuraren su dawo su ci gaba da aiki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta gaji ɗumbin matsaloli daga wajen gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta gaji tashoshin samar da ruwa da suka lalace waɗanda aka ɓarnata na miliyoyin Naira, daga gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Twitter
Kwamishinan ruwa na jihar, Hon. Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara tare da ƴan jarida domin dubawa da tantance tashoshin samar da ruwan, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano tushen ƙarancin ruwan jihar Kano
Gwamnatin ta ce wannan ne tushen matsalar ƙarancin ruwa da ake fama da ita a jihar.
Cikin wuraren da abin ya shafa har da tashar samar da ruwa ta farko da aka gina a Kano tun shekarar 1930, da kuma tashar samar da ruwa ta Challawa da tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gina.
Gwamnatin Kano ta nuna yatsa ga Ganduje
Kwamishinan ya nuna takaici kan yadda aka lalata wuraren, yana mai cewa dukkanin waɗannan wurare suna aiki yadda ya kamata har zuwa shekarar 2016, lokacin da gwamnatin Ganduje ta bar su babu kulawa.
Doguwa ya bayyana cewa kusan kilomita 12 na bututun ruwa da ke kawo ruwa daga Kogin Kano zuwa tashar samar da ruwa an tone su, yayin da ɗakin kula da na'urori da famfunan ruwa na farko aka lalata su kuma aka sace.
Ya ƙiyasta cewa gwamnati za ta kashe kimanin dala miliyan 10 domin gyarawa da dawo da waɗannan wurare su koma aiki.
"Tashar samar da ruwa ta farko an gina ta ne a shekarar 1930, tana aiki har zuwa 2016, amma an lalata ta a lokacin gwamnatin da ta gabata. An kiyasta ɓarnar da aka yi a kai zuwa dala miliyan 3.5.”
“Wannan tasha na da ƙarfin tace lita miliyan 20 na ruwa a kullum, kuma lalacewarta ta haddasa mummunan karancin ruwa a fadin jiha."
- Umar Haruna Doguwa

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa tashar samar da ruwa ta Intel 6 da Gwamna Kwankwaso ya kafa na da ikon samar da lita miliyan 350 na ruwa a kullum, wato rabin abin da Kano ke buƙata a kullum.
Doguwa ya nuna baƙin ciki cewa an yi wa tashar ɓarna da gangan a shekarar 2016, inda famfuna da kowannensu ke da darajar sama da Naira miliyan 500 aka sayar da su.
Gwamnatin Abba ya yi naɗe-naɗe a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.
Gwamna Abba ya naɗa Malam Haladu Mohammed a matsayin mai ba da shawara na musamman a kan inganta ilmi.
Hakazalika Gwamna Abba ya amince da naɗin Muhammad Inuwa Jika a matsayin mataimaki na musamman kan gyaran kayan sadarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng