Ana Raɗe Raɗin Sauya Shekar Kwankwaso, Ƴan NNPP da PDP Sama da 200 Sun Koma APC
- Gwamna Umar Namadi ya karɓi mambobin jam'iyyun NNPP da PDP sama da 200 waɗanda suka rungumi APC nai mulki a jihar Jigawa
- Masu sauya sheƙar sun bayyana cewa salon jagorancin gwamna da ayyukan alherin da ya yi masu ne suka jawo hankalinsu zuwa APC
- Gwamna Namadi ya tarbe su hannu bibbiyu a wani taro da kungiyar haɗakar ƴan kasa da gwamnati ta shirya a ƙaramar hukumar Gagarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jigawa - Akalla mambobi 216 na jam’iyyun PDP da NNPP ne suka sauya sheƙa daga jam’iyyunsu zuwa APC a karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa.
An karɓi masu sauya shekar ne a hukumance a wani taro da kungiyar “Citizens and Government Engagement Forum" ta shriya a hedikwatar karamar hukumar.

Asali: Twitter
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da wasu manyan jami’an gwamnati sun halarci taron, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Namadi ya buɗe kunnen sauraren koke
A yayin taron, Gwamna Namadi ya ce an kirkiri ƙungiyar ne domin bai wa ’yan jihar damar jin abubuwan da gwamnati ta cimma cikin shekaru biyu da suka wuce da kuma shirinta na gaba.
Hakanan, ya ce kungiyar ta bai wa jama’a damar gabatar da korafe-korafensu da bukatunsu domin gwamnati ta san halin da ake ciki kuma ta kai daukin gaggawa.
Gwamna Namadi ya jaddada cewa ƙofar kungiyar a bude take ga kowane dan jihar Jigawa, kuma ba dole sai ɗan jam'iyyar APC ba.
Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta saurari korafe-korafe na gaskiya da shawarwari masu ma’ana.
Umar Namadi ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen ci gaba domin inganta rayuwar al’umma da makoma mai kyau a jihar Jigawa.
Wane ci gaba aka samu a jihar Jigawa?
A yayin taron, kwamishinoni shida daga ma’aikatun daban-daban sun gabatar da jerin ayyukan da aka aiwatar a karkashin gwamnatin Gwamna Namadi.
Wadannan ayyuka sun hada da gina tituna, shirye-shiryen tallafawa jama’a, gyaran asibitoci ciki har da Asibitin Gagarawa da aka kusa kammala wa, da shirin samar da ayyukan da tallafin karatu.

Asali: UGC
Da yake magana da yawun masu sauya sheka, Malam Habibu Dangodo ya mika jerin sunayensu ga shugaban APC na jihar Jigawa, Hon. Aminu Sani Gumel.
Dangodo ya bayyana cewa shugabancin Gwamna Namadi mai hangen nesa ne ya ja hankalinsu suka yanke shawarar sauya sheƙa zuwa APC.
“Shugabancin Gwamna Namadi ya tabbatar mana cewa APC na da kyakkyawar manufa ga karamar hukumar Gagarawa da Jihar Jigawa baki daya.
"Hakan ya sa muka ga dacewar hada kai da shi domin gina Jigawa,” in ji Dangodo.
APC ta karɓi manyan ƴan adawa a Sakoto
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ƙara samun karuwa a jihar Sakkwato da wasu manyan jiga-jigai suka sauya sheka zuwa cikinta.
Shugabar matan PDP a mazaɓar Sakkwato ta Tsakiya, Hajiya Ummu Gada, ce ta jagoranci masu sauya sheƙar zuwa APC mai mulki.
Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai jagorar mata ta Kware, Hajiya Shafa Yusuf Kware da Zainab Ibrahim daga Sokoto ta Kudu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng