Tsohon Jigon APC Ya Fadi Yadda Mulkin Tinubu Ya Fusata Yan Najeriya Cikin Shekara 1

Tsohon Jigon APC Ya Fadi Yadda Mulkin Tinubu Ya Fusata Yan Najeriya Cikin Shekara 1

  • Masana suna cigaba bayyana ra'ayoyinsu kan yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shekara a kan mulki
  • Dakta Usman Bugaje ya bayyana ra'ayinsa inda yace Najeriya ta fuskanci matsaloli da dama a karkashin shugaba Tinubu
  • Ya kuma bayyana hanyoyin da za a bi domin ganin matsalolin ba su cigaba ba balle su kai ga durkushewar kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A cigaba da baje ra'ayoyi da masana ke yi kan yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cinye shekara kan karagar mulki, Dr Usman Bugaje ya tofa albarkacin bakinsa.

Tinubu
Dakta Usman Bugaje ya ce an sha wahala cikin shekara guda da Tinubu ya yi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Dakta Usman Bugaje ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaza cikin shekara daya da tayi tana juya akalar Najeriya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Ministoci na cikin matsala, Tinubu ya basu umarni kan ayyukansu

A kan haka ne Dakta Bugaje ya ce lallai ya kamata shugaban kasar ya nemi shawararin masana domin samun mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalolin da aka fuskanta a mulkin Tinubu

Dakta Usman Bugaje ya ce an fuskanci tarin matsalolin cikin shekarar da Bola Tinubu ya yi yana mulki.

Babbar matsalar da aka samu a cewar Dakta Bugaje ita ce tashin farashin kayayyaki wanda a halin yanzu ya fusata yan kasa.

Me ya kamata shugaba Tinubu ya yi?

Dakta Bugaje ya ce Allah ya albarkci Najeriya da masana sosai saboda haka shugaban kasar ya kamata ya nemo su domin su tallafa masa.

Ya kara da cewa idan har shugaban kasar zai samu masu tallafa masa wurin fitar da 'yan Najeriya a halin da suke ciki ko da daga wata jam'iyya ne ya kamata ya yi aiki da su.

Yadda wasu kasashe suka samu mafita

Kara karanta wannan

"Da wahala", Jigon APC ya gaji da kame kamen Tinubu wajen gyara Najeriya kamar Lagos

Dakta Bugaje ya ce kasashe da dama sun fuskanci irin matsalar da Najeriya ke ciki a halin yanzu kuma sun samu mafita, rahoton Punch.

Saboda haka ya bada shawara kan a nemo masu kishin kasa domin su tallafa wajen ganin Najeriya ba ta durkushe ba.

Bola Tinubu ba zai hana adawa ba

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta musanta zargin cewa shugaba Bola Tinubu na kokarin mayar da kasar tsarin jam'iyya daya tal.

Mashawarcin shugaba kasa na musamman kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyan haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel