Bayan Yin Garambawul, Gwamnan Nasarawa Ya Nada Sababbin Kwamishinoni
- Gwamnan jihar Nasarawa ya fara maye gurbin ƴan majalisar zartarwar da ya kora daga kan muƙamansu a kwanaki
- Abdullahi Sule ya naɗa sababbin kwamishinoni har mutum 16 waɗanda yake son ya yi aiki da su a gwamnatinsa
- Gwamnan ya miƙa sunayensu gaban majalisar dokoki domin tantance su kafin a tabbatar da su domin zama kwamishinoni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya naɗa sababbin kwamishinoni 16 da za su yi aiki a gwamnatinsa.
Gwamna Abdullahi Sule ya aika da sunayensu zuwa ga majalisar dokokin jihar don tantancewa tare da amincewa da su a matsayin kwamishinoni.

Asali: Facebook
Gwamna Sule ya naɗa kwamishinoni
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan a lokacin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa tsofaffin ƴan majalisa guda biyu da kwamishinoni shida da suka riƙe muƙamai a baya suna cikin jerin sunayen da Gwamna Sule ya miƙa.
Haka kuma, mata uku sun samu shiga cikin jerin sunayen na mutum 16 da aka gabatar a gaban majalisar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa daga cikin waɗanda aka naɗa akwai tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, Umar Tanko-Tunga, da kuma tsohon ɗan majalisa, Mohammed Agah-Muluku.
Kakakin majalisa ya ayyana jerin sunayen
“Gwamna ya aika da sunayen kwamishinoni 16 don tantancewa da amincewa da su."
"Don haka, ina kira ga waɗanda aka naɗa su kawo kwafi 30 na takardun tarihin karatunsu (CV) zuwa majalisa kafin ranar Alhamis. Sannan su bayyana don tantancewa a ranar Litinin mai zuwa."
- Danladi Jatau
Jerin Sunayen kwamishinonin da aka naɗa
- Yakubu Kwanta - Daga ƙaramar hukumar Akwanga
- Tanko Tunga - Daga ƙaramar hukumar Awe
- Munirat Abdullahi - Daga ƙaramar hukumar Doma
- Gabriel Agbashi - Daga ƙaramar hukumar Doma
- Barr. Isaac Danladi-Amadu - Daga ƙaramar hukumar Karu
- Princess Margret Itaki-Elayo - Daga ƙaramar hukumar Keana
- Dr. Ibrahim Tanko - Daga ƙaramar hukumar Keffi
- Dr. John DW Mamman - Daga ƙaramar hukumar Kokona
- Aminu Mu’azu Maifata - Daga ƙaramar hukumar Lafia
- CP Usman Baba (mai ritaya) - Daga ƙaramar hukumar Lafia
- Mohammed Sani-Ottos - Daga ƙaramar hukumar Nasarawa
- Mohammed Agah-Muluku - Daga ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon
- Barr. David Moyi - Daga ƙaramar hukumar Obi
- Dr. Gaza Gwamna - Daga ƙaramar hukumar Toto
- Barr. Judbo Hauwa Samuel - Daga ƙaramar hukumar Wamba
- Muazu Gosho - Daga ƙaramar hukumar Wamba
Gwamna Sule zai hukunta jami'an gwamnati
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna takaicinsa kan yadda aka sanya rashin gaskiya a shirin ɗaukar malamai
Gwamna Sule ya bayyana cewa wasu daga cikin jami'an gwamnati da ta ɗora a kan aikin, sun riƙa karɓar kuɗi daga hannun mutane domin siyar da takardar ɗauki.
Ya bayyana cewa zai haɗa jami'an gwamnatin da hukumomin tsaro domin su ɗauki mataki a kansu kan rashin gaskiyar da suka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng