Abu Ya Yi Zafi: Mai Neman Takarar Gwamna a APC Ya Maka Jam'iyyar a Kotu kan Zaɓe
- Jigon APC, Valentine Ozigbo ya maka jam’iyyar a kotu kan zaben tsaida gwani na gwamna a Anambra, yana neman soke sakamakon
- Ozigbo ya zargi zaben da aka yi ranar 5 ga Afrilun 2025 da cewa cike yake da magudi da sunaye na bogi a cikin jerin wakilai
- Ya ce 'yan APC na gaske ba su samu damar shiga ba, kuma babu wani tsarin tantance wakilai, ya ce zaben yana cike da matsaloli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Wani daga cikin wadanda suka yi takara a zaben fitar da gwani na gwamna a APC ya maka jam'iyyar a kotu.
Valentine Ozigbo wanda da ya fafata a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a Anambra, ya kai kara kotu ne kan sakamakon zaben.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ɗan siyasar ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Juma'a 18 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya maka jam'iyya a kotu
'Dan siyasar ya shiga zaben fitar da gwani na APC da aka gudanar ranar 5 Afrilu 2025, wanda Nicholas Ukachukwu ya lashe da kuri’u 1,455.
Mista Ozigbo ya samu kuri’u 67 ne kawai, yayin da sauran ‘yan takara Edozie Madu da Johnbosco Onunkwo suka samu 8 da 26
A ranar 8 Afrilu, Mista Ozigbo ya rubuta korafi ga kwamitin daukaka kara na APC, yana kiran zaben da “zamba ce da shirme.”
A cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, Mista Ozigbo ya ce ya kai kara kotu domin kalubalantar “halaccin” zaben fidda gwanin APC.
Ya ce:
“Bayan mun kammala kokarin cikin gida na jam’iyya wajen daukaka kara kan taron wakilai da kuma zaben fidda gwani, sai na je kotu, ba wai don neman suna ba ba ne, amma domin kare adalci, gaskiya da bin ka’ida."

Asali: Facebook
Dalilin shiga kotu da 'dan APC ya yi
Ozigbo ya ce ba kawai batun takararsa ba ne, amma makomar jam’iyyar da kuma dimokuradiyya baki daya na cikin hadari.
Mista Ozigbo bai bayyana cikakken bayani kan karar ba, ciki har da kotun da ya shigar da ita.
Ya zargi zaben fidda gwanin APC da cewa 'ba gaskiya ba ne, an kirkiri jerin sunaye ne da ba a san su ba'.
Ya ce ‘yan jam’iyyar na gaskiya sun rasa damar shiga zaben, kuma ba a tantance wakilan zaben ba.
Ya ce:
“Babu tsari, sai bara-gurbi, tashin hankali da wasu yan hayar da aka ce su ne wakilai, an riga an rubuta sakamakon tun kafin zaben.”
Tsohon shugaban APC ya yi murabus
Kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya fice daga jam’iyyar saboda rikicewar shugabanci a jihar.
Nwoye ya ce ya tattauna da magoya bayansa kafin yanke shawarar barin jam’iyyar, amma bai fadi inda zai koma ba tukuna.
Jigon jam'iyyar ya zargi shugabancin APC a Kudu maso Gabas da siyasar ramuwar gayya da rashin niyyar kara samun wata jiha a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng