Tsohon Shugaban APC Ya Rikita Mata Lissafi bayan Yin Murabus, Ya Soki Salon Ganduje
- Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya fice daga jam’iyyar saboda rikicewar shugabanci a jihar
- Nwoye ya bayyana cewa ya tattauna da magoya bayansa kafin yanke shawarar barin jam’iyyar, amma bai fadi inda zai koma ba tukuna
- Ya zargi shugabancin APC a Kudu maso Gabas da siyasar ramuwar gayya da rashin niyyar kara samun wata jiha a yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Jam'iyyar APC reshen jihar Enugu ta samu koma baya bayan ficewar wani jigonta da ya ba da gudunmawa sosai.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar, Dr. Ben Nwoye, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Asali: Facebook
Tsohon shugaban APC ya yi murabus
Nwoye ya bayyana ficewarsa a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Alhamis, yana mai cewa rikicewar shugabanci ta sa ya fice, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin yanke shawarar, Nwoye ya ce ya tuntubi magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar siyasa a Enugu, sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.
Nwoye ya ce:
“’Yan tsintsiya da muka hada da wahala a 2013 lokacin da ake musu kallon banza sun watse gaba daya.
Ya ce shugabannin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Gabas suna gudanar da siyasar ramuwar gayya, ba sa son kara samun wata jiha, Leadership ta ruwaito.
A cewarsa:
“Shugabancin APC a Kudu maso Gabas na cikin siyasar ramuwar gayya, ba sa son samun wata jiha bayan guda biyu da muke da su.
“A wurinsu, karfin jam’iyya yana nufin yadda za su ci zarafin wadanda suka dauka a matsayin abokan adawa a jam’iyya.
“Suna wulakanta muhimman ka’idojin APC wato adalci, zaman lafiya da hadin kai, gaskiya ne, sun bace daga hanya."

Asali: Facebook
Zarge-zargen da Nwoye ya yi ga Ganduje
Nwoye ya kuma zargi shugabannin jam'iyyar APC na kasa da jin dadin mulki, saboda su ke da shugaban kasa da yawancin ‘yan majalisar tarayya.
“Shugabannin APC na kasa sun ki ganin gaskiya, suna barin bangarori su lalata juna har jam’iyyar ta durkushe a jihar Enugu.
“Abin takaici, suna wulakanta kiran dattawan jam’iyya na neman sulhu, kuma suna daukar masu neman hadin kai a matsayin ƴan son banza..
“Na yi tuntuba sosai da magoya bayana a kasa, kuma na yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zan ci gaba, ba bawa bane ni.
“Ban taba zama bawan siyasa ba, kuma ba zan taba zama ba."
- Cewar Nwoye
'Dan majalisa ya bar PDP zuwa APC
A baya, mun ba ku labarin cewa jam’iyyar PDP ta sake fuskantar koma baya a jihar Edo bayan dan majalisar dokoki, Nicholas Asonsere ya sauya sheka zuwa APC.
Asonsere ya bayyana cewa ayyukan alheri da Gwamna Monday Okpebholo ke yi ya karfafa masa gwiwar barin PDP don marawa ci gaban yankinsa baya.
Hakan ya biyo bayan bugan kirji da shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi cewa za su kwace wasu jihohi.
Asali: Legit.ng