Za a Canza Tinubu?" Hon. Farouk Aliyu Ya Faɗi Wanda APC Za Ta ba Takara a 2027

Za a Canza Tinubu?" Hon. Farouk Aliyu Ya Faɗi Wanda APC Za Ta ba Takara a 2027

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne zai sake yin takara karo na biyu a inuwar jam'iyyar APC a babban zaɓen 2027 mai zuwa
  • Tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Hon. Farouk Aliyu ne ya fadi hakan a wata hira da aka yi da shi
  • Ya kuma taɓo batun ficewar Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP, yana mai cewa ya ba da gudummuwa ga nasarar Tinubu a 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da ake ta zancen babban zaben 2027, tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Adamu Aliyu ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ɗan takarar APC.

Farouk Aliyu, tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai ta ƙasa, ya ce Bola Tinubu ne zai sake takarar shugaban ƙasa a inuwar APC a zaɓen 2027.

Shugaba Tinubu.
Tsohon dan majalisa, Farouk Aliyu ya ce Tinubu ne zai ƙara takara a inuwar APC a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hon. Farouk ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin 'siyasa a yau' na tashar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A jam’iyyarmu watau APC, muna da dan takararmu kuma shi ne Shugaban kasa. Babu wata matsala a kan haka. Mun san dan takararmu kuma za mu yi aiki don ganin ya ci zaɓe da ikon Allah.”

Farouk Aliyu ta taɓo batun Nasir El-Rufai

Farouk Aliyu ya tabo batun ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyyar APC, yana mai tunawa da irin rawar da ya taka a APC.

Tsohon ɗan Majalisar ya jaddada cewa El-Rufai ya tallafa wa Bola Tinubu har ya kai ga samun nasara a zaben 2023.

Ya ce Nasir El-Rufai ne ya jagoranci gwamnonin Arewa wajen goyon bayan Tinubu, har ya tozarta wasu don tabbatar da nasarar shugaɓan ƙasa a zaben a zaɓen da ya gabata.

Wace irin gudumnuwa El-Rufai ya ba Tinubu?

El-Rufai na daga cikin jiga-jigan siyasa daga Arewa da suka dage cewa jam’iyyar APC ta mika tikitin takarar shugaban kasa ga dan kudu a zaben 2023, bisa tsarin karba-karba da ba a rubuta ba.

A matsayinsa na Gwamnan Kaduna daga 2015 zuwa 2023, El-Rufai ya nuna goyon bayansa ga tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu.

Duk da haka, bayan nasarar Tinubu da kafa gwamnati, El-Rufai bai samu mukamin minista ba, wanda ake zargin hakan ya jawo saɓani tsakaninsu har ya bar APC zuwa SDP.

Nasir El-Rufai.
Hon. Farouk Aliyu ya bayyana gudummuwar da El-Rufai ya ba Shugaba Tinubu Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Da yake tsokaci kan El-Rufai, Hon. Farouk Aliyu ya ce:

“Abokina Nasir El-Rufai ya fito fili lokacin da Bola Tinubu ke son zama Shugaban kasa, ya jagoranci gwamnonin Arewa, ya fadi albarkacin bakinsa.
"Mun bi shi, mun bi Tinubu har ya ci zabe. An yi masa alkawarin mukamin minista, amma wani abu ya faru, bai samu ba."

2027: Za a fafata tsakanin ƴan Najeriya da APC

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa zaɓen 2027 zai gudana ne tsakanin ƴan Najeriya da jam'iyyar APC.

Gwamna Makinde na jihar Oyo ya ce PDP ba za ta yi wata wahala ba domin ƴan Najeriya ne ke da wuka da damar yanke hukukci a fagen zaɓe.

A cewarsa, PDP ita ce fatan talaka, yana mai tabbatar da cewa PDP ba za ta sake kuskuren da ya sa ta faɗi zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262