PDP Ta Gamu da Matsala a Sokoto, Shugabar Mata da Manyan Jam'iyyar Sun Koma APC

PDP Ta Gamu da Matsala a Sokoto, Shugabar Mata da Manyan Jam'iyyar Sun Koma APC

  • Hajiya Ummu Gada, jagorar mata ta PDP a Sokoto ta Tsakiya, ta sauya sheka zuwa APC tare da wasu jiga-jigan PDP daga yankin
  • Ta zargi PDP da rashin adalci da girmama mambobinta, inda ta ce an mayar da jam’iyyar tamkar ƙungiyar asiri da babu tsarin dimokuraɗiyya
  • Shugaban PDP a jihar, Bello Goronyo, ya ce sauya shekar ba zai shafi jam’iyyar ba, yana mai jaddada ‘yancin kowa ya bar jam’iyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Jagorar mata ta jam’iyyar PDP a yankin Sokoto ta Tsakiya, Hajiya Ummu Gada, ta sauya sheka zuwa APC tare da wasu 'yan PDP daga yankin.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai jagorar mata ta Kware, Hajiya Shafa Yusuf Kware, da Zainab Ibrahim daga Sokoto ta Kudu.

Shugabar mata a Sokoto ta fadi dalilin sauya sheka daga PDP zuwa APC
Shugabar mata a Sokoto, Hajiya Umu Gada da tawagarta a ofishin jam'iyyar APC. Hoto: Abubakar Umar Danmaisallah
Asali: Facebook

Sauran wadanda guguwar sauya shekar Hajiya Ummu Gata ta tafi da su APC akwai shugaban matasa na Kware, Alhaji Buhari Abubakar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sokoto: Shugabar mata ta fice daga PDP

Da take sanar da sauya shekar su a ofishin APC da yammacin Alhamis, Hajiya Gada ta zargi PDP da nuna halin ko in kula ga mambobinta da rashin tafiya da tsarin dimokuraɗiyya.

“Na fice ne saboda PDP ba ta daraja mambobinta. An mayar da jam’iyyar tamkar ƙungiyar asiri,” inji Hajiya Gada.

Ta kuma danganta sauya shekar nata da ci gaban da Gwamna Ahmed Aliyu (wanda ta kira da 'kina') ke samu a jihar Sokoto.

Yayin da ta ce gwamnan ya sauya fasalin jihar, shugabar matar ta ce:

“Sokoto ta fara komawa kamar Dubai saboda gagarumin aikin da ake yi. Gwamna yana cika alkawuran da ya ɗauka. Ya kara albashi kuma yana biya a kan lokaci."

Hajiya Gada ta bayyana kwarin gwiwar cewa akwai karin mambobin PDP da za su sauya sheka zuwa APC daga dukkan kananan hukumomi 23 na jihar.

“Jam'iyyar APC ce asalin inda ta dace da ni. Kaddara ce ta kai ni PDP, amma yanzu na dawo gida,” inji shugabar mata, Hajiya Gada.

APC ta yi maraba da shugabar mata a Sokoto

Ta kuma roki afuwa daga tsohon gwamna kuma jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, saboda barin jam’iyyar da ta yi a baya.

Shugabar matan ta roki Sanata Wamakko da cewa:

“Ina rokon ubanmu kuma jagoranmu, Sanata Wamakko, da ya yafe mini. Duk abin da na zama a yau, silar jagorancin sa ne. Don Allah ka yafe wa ‘yar ka."

Da yake karɓar masu sauya sheka, Shugaban APC na jihar, Alhaji Isa Sadiq Achida, ya tarbe su hannu bibbiyu, ya kuma tabbatar musu da samun kulawa a jam’iyyar.

Masu fashin baki sun bayyana wannan sauya sheka a matsayin babban karuwa ga APC a jihar Sokoto, da zai ƙara ƙarfafa tushen siyasar jam’iyyar.

PDP ta mayar da martani kan sauya shekar

Shugaban PDP a jihar Sokoto, Hon. Bello Goronyo, ya yi kokarin karya tasirin sauya shekar da jiga-jigansu suka yi, yana mai cewa hakan ba zai shafi karfin jam’iyyar ba.

A martaninsa, Goronyo ya ce wadanda suka fice ba su sanar da jam’iyyar ba a hukumance, illa kawai sun ga labarin a kafafen sada zumunta.

Yayin da ya jaddada cewa PDP ba ta damu da sauya shekar ba, ya ce:

“Ba za mu zarge su da komai ba. A siyasa, kowa yana da ‘yancin ya zauna ko ya fice daga jam’iyya."

Tsohon shugaban APC ya yi murabus

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban APC a Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar sakamakon rikicin shugabanci.

Nwoye ya ce ya yi dogon nazari tare da shawarwari da magoya bayansa kafin daukar matakin, sai dai bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba tukuna.

Ya zargi shugabannin APC na Kudu maso Gabas da nuna son zuciya da rashin kishin jam’iyya, yana mai cewa siyasar ramuwar gayya ce ke hana jam’iyyar ci gaba a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.