2027: El Rufa'i, Al Mustapha Sun Karbi Sanata Ubale Shitu zuwa SDP a Abuja
- Sanata Muhammad Ubale Shitu daga jihar Jigawa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP a wani gagarumin taro da aka gudanar a birnin Abuja
- Manjo Hamza Al-Mustapha da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun halarci taron, abin da ya kara girman lamarin a fagen siyasa
- Shugaban SDP, Shehu Musa Gabam, ya ce sauya shekar Sanata Shitu alama ce da ke tabbatar da karfin gwiwa a kokarin kawo sauyi a kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An kafa tarihi a hedkwatar jam’iyyar SDP da ke Abuja yayin da tsohon mataimakin gwamnan Jigawa, Sanata Muhammad Ubale Shitu ya koma SDP.
Sauya shekar ta kasance babban sauyi a tafiyar siyasar SDP a Najeriya, musamman a lokacin da take kokarin tasowa da karfinta.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da jam'iyyar SDP ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Shitu ya samu rakiyar Major Dr Hamza Al-Mustapha, yayin da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kasance cikin mahalarta taron.
Shugaban SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ya mika wa Sanata Shitu katin shaidar zama dan jam'iyya.
Gabam ya ce SDP na kara karfi a Najeriya
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa jam’iyyar SDP na kara karɓar ’yan siyasa masu nagarta da kwarewa, abin da ke kara mata farin jini a idon jama’a.
Ya ce:
“Mun kuduri aniyar gina Najeriya bisa gaskiya da adalci, kuma sauya shekar Sanata Shitu wata shaida ce ta cewa SDP na karɓar shugabanni masu kishin kasa.”
Ya kara da cewa SDP na kokarin gina kasa mai adalci, wacce za ta bai wa kowa dama bisa cancanta ba tare da nuna bambanci ba.

Asali: Facebook
Al-Mustapha ya yi kira ga ’yan Najeriya
A jawabinsa, Major Dr Hamza Al-Mustapha ya yi kira ga dukkan ’yan Najeriya da su hada kai da jam’iyyar SDP domin ceto kasa.
Ya ce Najeriya na cikin halin tsananin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, kuma lokaci ya yi da za a nemi mafita ta gaskiya.
Ya bayyana SDP a matsayin jam’iyya mai cike da hangen nesa da adalci, wadda ke da shirin jagorantar Najeriya zuwa tudun mun tsira.
Hamza Al-Mustapha ya ce:
“Wannan kira ba na siyasa kawai ba ne, kira ne na kasa. Mu hadu mu dawo da mutuncin Najeriya domin ceto makomar ‘ya’yanmu.”
Ya kara da cewa lokaci ya yi da ’yan Najeriya za su tashi tsaye su rungumi jam’iyyar da ke da gaskiya da kishin kasa, domin dawo da martabar kasa.
Shugabannin APC sun koma SDP a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar SDP ta kara karfi yayin da ta karbi wasu shugabannin APC da NNPP a Kaduna.
Shugabannin jam'iyyun biyu da ke wata mazaba a karamar hukumar Kubau ne suka sauya sheka baki daya suka koma SDP.
Ana ganin sauya shekar Nasir El-Rufa'i na cikin dalilan da suke sanya jam'iyyar kara karfi a Najeriya, musamman a Jihar Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng