Doguwa ya bayyana dalilin da yasa jigogin PDP a Kano suka raba jaha da Kwankwaso

Doguwa ya bayyana dalilin da yasa jigogin PDP a Kano suka raba jaha da Kwankwaso

Tsohon shugaban tsagin jam’iyyar PDP ta jahar Kano, Mas’ud El-Jibril Doguwa ya bayyana babban dalilin da yasa jiga jigan jam’iyyar PDP reshen jahar Kano suka yi fatali da jam’iyyar tare da yin hannun riga da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Doguwa yana fadin cewa sun dauki matakin ficewa daga jam’iyyar ne sakamakon farin jininta ya kare a wajen al’ummar jahar Kano, don haka yasa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, yayin da zaben gwamnoni da yan majalisu ya rage saura kwanaki biyar kacal.

KU KARANTA: Murnar samun nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja

Doguwa ya bayyana dalilin da yasa jigogin PDP a Kano suka raba jaha da Kwankwaso
Doguwa da Kwankwaso
Asali: UGC

Doguwa ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da yan jaridu a ranar Litinin, 4 ga watan Maris a garin Kano, inda yace jam’iyyar PDP ta rasa karsashinta a matsayin jam’iyyar adawa sakamakon mayar da shuwagabanninta saniyar ware a jam’iyyar.

Doguwa ya cigaba da cewa rashin hadin kai da kuma kyakkyawar manufa ta janyo tashin tashinan da jam’iyyar take fama dashi a yanzu,don haka yace ba za’a taba cimma nasarar da ake bukata a jam’iyyar ba matukar ba’a daina mulkin kama karya ba.

“Tun lokacin da dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP ya bayyana, bai taba kiranmu akan yadda za’a tafiyar da jam’iyyar ba, kuma duk matakin da muka yi kira a dauka don kawo tsafta a siyasar cikin gida ba’a amfani dashi.

“Hakan ba zai haifa ma jam’iyya da mai ido ba, PDP ta rasa alkiblan fuskanta, farin jininmu ya dusashe a kafatanin kananan hukumominmu 44, don haka muka fice daga cikinta, ficewar jiga jigan yayanta ya nuna PDP zata sha kayin da ba zata taba farfadowa ba.” Inji shi.

Daga karshe Doguwa yayi ha sashen jam’iyyar APC da dan takararta a zaben gwamnan jahar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zasu samu gagarumar nasara a zaben gwamnoni da yan majalisu da za’ayi a ranar 9 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel