"Yadda Muka Yaki Zancen Magudin Zabe a 2023, Aka Wanke Tinubu," Ministan Buhari

"Yadda Muka Yaki Zancen Magudin Zabe a 2023, Aka Wanke Tinubu," Ministan Buhari

  • Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayyana cewa ta fuskanci zarge-zarge na cewa ta bari an yi magudi a zaɓen 2023
  • An samu masu shakku a kan sahihancin zaɓen da ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya
  • Tsohon Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce sun rika wayar da kan kafafen yada labaran kasar waje a kan zargin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Tsohon Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce gwamnatinsu ta tuntubi kafafen yada labarai na ƙasashen waje domin ƙaryata jita-jitar cewa an yi magudi a zaben 2023.

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron kolin tsofaffin masu magana da yawun gwamnati da aka gudanar a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan mutum 54: Bincike ya jefo shakku a adadin wadanda aka hallaka a Filato

Tinubu
Ministan Buhari ya ce Tinubu ya ci zabe a Najeriya Hoto: Professor Isa Ali Pantami/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon Ministan ya tuna cewa bayan kammala zaben shugaban ƙasa na 2023, ya kai ziyara zuwa ƙasashe daban-daban domin karyata jita-jitar cewa an tafka magudi a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Buhari ya karyata magudin zaben 2023

Lai Mohammed ya bayyana cewa rahotannin da ake yadawa cewa Bola Tinubu ya lashe zaben ne ta hanyar magudi ba su da tushe balle makama.

Ya ce:

“Zarge-zargen magudi sun fara yaduwa ne sakamakon jinkirin da aka samu wajen lodin sakamakon zabe a shafin IReV — wanda a gaskiya, ba shi ne ginshiki a cikin tattara sakamakon zabe ba.
“Na jagoranci tawagata zuwa Birtaniya da Amurka domin ganawa kai tsaye da manyan kafafen yada labarai na waje da cibiyoyin nazari. Manufarmu ita ce mu gabatar da tabbatattun hujjoji kan yadda zaɓen ya gudana, da yadda aka ci zaben da yadda aka sha kaye.
“Mun gana da ‘yan jarida da wakilan Voice of America, The Washington Post, Foreign Policy Magazine, Associated Press, BBC, The Economist, Reuters, Bloomberg, Politico, Hudson Institute, U.S. Institute of Peace, Atlantic Council da Chatham House da sauransu."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fusata da gwamnan Binuwai ya yi masa korar kare

Gwamnatin Buhari ta wayar da kai a kasashen waje

Ya ce mafi yawan cibiyoyin da suka gana da su ba su da cikakken fahimta game da yadda tsarin kundin tsarin mulkin Najeriya ke tafiyar da nasarar zaben shugaban ƙasa.

Ya ce:

“Mun yi bayani cewa, a karkashin Sashe na 134, babi na 6 a Kundin Tsarin Mulki, dole ne dan takara ya ci kuri’u mafi yawa tare da samun 25% na kuri’u a akalla jihohi biyu bisa uku daga cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.
“Daga wannan sharadi, mun bayyana cewa ba PDP ba LP ba, babu ɗaya daga cikinsu da ke da hanyar cin zaben. Mun gabatar da cikakken bayani: dan takarar LP ya zo na uku da tazarar kusan kuri’u miliyan 2.7 tsakaninsa da dan takarar APC.
Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Lai Mohammed ya kara da cewa:

“Dan takarar APC ba kawai ya fi samun yawan kuri’u ba ne, har ila ya samu 25% na kuri’u a jihohi 29 — wanda ya haura ka’idar da tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi ainihin abin da ya kai Bola Tinubu Faransa

“Domin ƙara kawar da zargin magudi, mun gabatar da hujjojin da ba za a musanta ba: jam’iyyar APC ta sha kaye a muhimman jihohi masu yawan masu kada kuri’a — Lagos, Kaduna, Kano da Katsina — duk da cewa APC ke mulki a waɗannan jihohi.”

Zaben 2027: Tsohon Minista ya hango faduwa

A baya, kun samu labarin cewa tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya yi magana kan siyasar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, yana mai cewa akwai matsala.

Tsohon ministan ya ce ba zai iya tabbatar da ko Tinubu zai yi nasara ko akasin haka a zaɓen 2027 ba, amma yana da tabbacin cewa ‘yan Najeriya sun san yadda za su tunkari zaben.

Dalung ya kwatanta halin da Tinubu ke ciki da irin matsalolin da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya fuskanta a 2015, wanda ya haifar da rashin nasararsa a wancan lokacin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng