Bututun Mai Ya Fashe a Rivers Ana tsaka da Zancen Tsige Gwamna Fubara
- Wani abin fashewa ya fashe a bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP) da ke Bodo, karamar hukumar Gokana, Jihar Rivers
- Rahotanni sun nuna cewa gobara ta barke a yankin da abin ya faru a jihar, inda bakin hayaki ke tashi zuwa sararin samaniya
- Hukuma ba ta tantance musabbabin fashewar ba, sai dai ana zargin yiwuwar hannun ‘yan bindiga masu barazanar kai hari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Fashewar bam ya girgiza bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP) da ke Jihar Rivers, lamarin da ya haddasa babbar gobara.
Bayanai sun nuna cewa fashewar ta faru ne da daddare a ranar Litinin, amma har zuwa safiyar Talata, wuta na ci gaba da ci a yankin.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa har yanzu hukumomi ba su tabbatar da musabbabin fashewar ba, amma ana zargin cewa yana da nasaba da barazanar hare-hare da wasu ‘yan bindiga suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobara ta barke tarwatsewar abin fashewa
Wata babbar gobara ta barke bayan fashewar da ta auku a bututun mai na TNP, inda hayaki mai kauri ya cika sararin sama.
Wani bidiyo da ya bayyana a safiyar Talata ya nuna wutar na ci gaba da bazuwa cikin dazukan da ke yankin.
Rahoton Leadership ya nuna cewa bututun man na daga cikin mahimman hanyoyin jigilar mai zuwa tashar Bonny Export Terminal da ke Jihar Rivers.

Asali: Facebook
Fashewar ta haddasa tashin hankali a yankin, inda jama’a ke cikin firgici kan abin da zai biyo baya.
Ana zargin da hannun ‘yan bindiga a harin
Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da musabbabin fashewar ba, amma ana fargabar hannun ‘yan bindiga masu tada kayar baya a ciki.
A ‘yan makwannin nan, wasu kungiyoyin ‘yan bindiga sun yi barazanar kai hare-hare kan kadarorin man fetur a yankin.
Wannan barazana ta zo ne sakamakon rikicin siyasa da ya dabaibaye Jihar Rivers, inda aka dakatar da tura kudin wata-wata na jihar.
Tun bayan barkewar rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon gwamna Nyesom Wike, an shiga wani hali na rashin tabbas a Rivers.
'Yan sanda sun ce ba su da cikakken bayani
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Rivers, Grace Iringe-Koko, ta ce ba ta da cikakken bayani kan lamarin.
Ta ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin fashewar da kuma yin tanadin tsaro a yankin da abin ya faru.
Har yanzu ba a bayyana asarar da gobarar ta haddasa ba, amma jama’an yankin sun shiga fargaba kan abin da zai biyo baya.
A halin yanzu, ana jiran karin bayani daga hukumomin tsaro da kamfanonin mai da ke aiki a yankin.
Fubara ya yi martani ga majalisar Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Siminalayi Fubara ya yi martani ga 'yan majalisar jihar masu biyayya ga Nyesom Wike kan barazanar tsige shi.
Gwamna Fubara ya bayyana cewa har yanzu bai karbi takardar tuhume tuhume da majalisar ta ce ta tura masa kan zarge zargen yunkurin tsige shi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng