Majalisar Tarayya Ta Kare Matakin Sauke Gwamnatin Ribas na Watanni 6
- Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana cewa sai da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da 'yan majalisa kafin daukar matakin soji a Ribas
- A yammacin Talata ne Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Ribas biyo bayan rashin jituwar siyasa tsakanin gwamna da 'yan majalisunsa
- Mai magana da yawun majalisar wakilai, Akin Rotimi, ya bayar da tabbacin cewa za a karanta wasikar da shugaban kasa ya aika masu a ranar Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Majalisar wakilan kasar nan ta ce shugaba Bola Tinubu ya tattauna da majalisar dokoki kafin ya sa dokar ta baci a jihar Ribas.
A yammacin ranar Talata ne shugaban kasa ya ayyana dokar ta baci a Ribas sakamakon rikicin siyasa da ya ki ci, ya ki cinye wa a jihar.

Asali: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mayaimakiyarsa, da kuma 'yan majalisar dokokin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa ya nada Ibok-Ete Ibas, tsohon mataimakin janar na ruwa, a matsayin shugaban gudanarwar jihar Ribas.
Ribas: Majalisar tarayya ta kare gwamnatin Tinubu
The Nation ta wallafa cewa a jawabinsa, mai magana da yawun majalisar wakilai, Akin Rotimi ya ce majalisar kasa tattauna da shugaban kasa kafin a dauki matakin bayyana dokar ta bacin.
Ya ce Tinubu ya gana da shugabannin majalisar kasa, ciki har da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio; da kuma shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen.

Asali: Facebook
Sauran wadanda suka halarci zaman sun hada da Benjamin Kalu, Mataimakin Shugaban Majalisar wakilai da Michael Bamidele, Shugaban Masu rinjaye a Majalisar Dattawa.
Sauran kuma su ne: Julius Ihonvbere, shugaban majalisar wakilai sai kuma Nuhu Ribadu, mai ba da shawara kan tsaro na kasa (NSA).
Tinubu ya gana da shugabannin tsaro kan Ribas
Rotimi ya ce Kayode Egbetokun, Sufetan 'yan sanda na kasa, Adeola Ajayi, Darekta janar na hukumar tsaron farin kaya, da Mohammed Mohammed, Darekta janar na hukumar bincike na kasa sun halarci zaman.
Ya ce:
“A yayin wannan taron, an sanar da su dukkanin manufar shugaba Tinubu, kuma dukkan wadanda suka halarta sun bayyana goyon bayansu ga matakin da aka dauka."
Majalisa za ta karanta wasikar Tinubu
Mai magana da yawun Majalisar wakilai, Akin Rotimi ya kara da cewa wasikar Tinubu da ta sanar da majalisar wakilai game da wannan shawara da neman amincewa ya na kan turba.
Ya ce shugaban kasa ya na da damar sanar da dokar ta baci a jihar Ribas a karkashin sashe na 305 na kundin tsarin mulki, wanda tuni bukatar shugaban ke gabanta.
Hon. Rotimi ya tabbatar da cewa majalisar dokoki ta kasa za a karanta wasikar a zamanta da za a gudanar na ranar Laraba don ci gaba da bin doka da oda.
Tinubu: Fubara ya tausashi al'ummar Ribas
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya roki al'ummar jihar su zauna lafiya kuma su ci gaba da bin doka duk da sanar da dakatar da shi da shugaban kasa ya yi.
Fubara ya ce tun lokacin da ya hau mulki a matsayin gwamna, ya yi kokarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma, musamman wajen tabbatar da tsaro da inganta walwalar mutanen Ribas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng