An Sake Rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da Gwamnonin PDP Sun Shirya Raba Shi da Mulki
- Da alama jam'iyyun adawa a Najeriya sun yunkuro domin kokarin tumbuke Bola Tinubu a zaben 2027 da za a yi nan da shekaru biyu
- Jam’iyyar NNPP da dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, na tattaunawa da wasu jam’iyyu don kifar da APC a 2027
- Shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP, Sanata Bala Mohammed ya nuna shirinsa na yin aiki da dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi
- Duka wannan bai rasa nasaba da shirin yan adawa domin ganin an yi wa Bola Tinubu da gwamnatinsa illa a babban zabe mai zuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Yayin da ya rage saura shekaru biyu a gudanar da zaben 2027, wasu jam'iyyun adawa sun fara shiri.
Jam'iyyun da ake ganin ka iya haɗewa sun hada da NNPP da PDP da LP da kuma SDP kawai domin kwace mulkin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da Peter Obi, gwamnan Bauchi ya bayyana shirin kifar da Tinubu a 2027

Asali: Facebook
Bala Mohammed ya yi zama da Peter Obi
Punch ta ruwaito cewa kakakin yada labarai na kasa na NNPP, Ladipo Johnson, ya tabbatar mata da shirinsu kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Peter Obi ya gana da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a gidan gwamantin jihar.
A cikin bayanansa, Gwamna Bala ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Obi saboda kwarewarsa a bangaren adawa.
Gwamnan wanda shi ne shugaban gwamnonin PDP a Najeriya ya ce kasar na buƙatar shugabanci nagari domin ceto al'ummarta.
Hakan ya jawo hasashe kan zaben 2027 da ake ganin ka iya zama shekarar da za a buga siyasa fiye da shekarun baya, cewar Vanguard.

Asali: Facebook
Matsayar NNPP da Kwankwaso kan hadaka
Kakakin NNPP, Johnson ya ce jam’iyyar da dan takararta na 2023, Rabiu Kwankwaso, na tattaunawa da wasu jam’iyyu domin kifar da Tinubu.
Ya bayyana cewa jam’iyyar na yin taka-tsantsan wajen kokarin hada kai, yana mai cewa sanarwa za ta fito idan lokaci ya yi.

Kara karanta wannan
Ana tsakiyar batun El Rufai, Peter Obi ya sa labule da Gwamna Bala kan dalilai masu ƙarfi
Ya ce:
“Toh, kamar yadda kuka sani, fagen siyasa a Najeriya yana da fadi, abin da zan iya tabbatarwa shi ne cewa jam’iyya, har da shugabanmu, Rabiu Kwankwaso, suna tattaunawa da mutane daban-daban da kungiyoyi, kuma har yanzu suna kokarin tuntubar wasu.”
“Yawancinmu a cikin ‘yan adawa mun fahimci cewa jama’ar kasa na fama, kuma dole mu hade ta kowace hanya domin dakile wannan gazawar tattalin arziki da sauran matsaloli.”
“Abin da nake cewa yanzu shi ne, ba lallai bane duk jam’iyyun adawa su hau mota daya, amma muna kokarin ganin cewa mu hada adawa mai karfi wadda za ta jagoranci wasu don kifar da gwamnati mai ci."
Da aka tambaye shi ko NNPP za ta sadaukar da kanta ga kowace dandalin hadin gwiwar jam’iyyun adawa, Johnson ya ce lokaci ne zai nuna.
El-Rufai ya watsar da jam'iyyar APC
Tun farko, mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP mai hamayya.
El-Rufai ya jero dalilai da suka hada da na rashin daidaito a tafiyar siyasa kamar yadda ya fadi a wata sanarwa a shafinsa na Facebook.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng