Abin da Abba Kabir Ya Fadawa Malamai da Ya Faranta Musu Rai yayin Buda Baki a Kano

Abin da Abba Kabir Ya Fadawa Malamai da Ya Faranta Musu Rai yayin Buda Baki a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi bakuncin manyan malamai domin buda baki a ranar Asabar, yana jaddada muhimmancin hadin kai da ci gaban addini
  • Gwamnan ya sanar da shirin sauya filin Idi na Kofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa don harkokin addini da ilimi
  • Za a kafa harsashin ginin cibiyar makonni biyu bayan Sallah, sannan a mika ta ga malamai domin tafiyar da ita yadda ya dace
  • Gwamna Yusuf ya yabawa addu'o’i da jagorancin malamai, yana rokon su da su ci gaba da hada kan al'umma da wanzar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafa hadin kai da ci gaban addini.

Gwamnan ya fadi haka ne yayin da ya karbi manyan malamai da limamai domin buda baki a gidan gwamnati ranar Asabar 15 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Albarkacin azumi: Yadda almajirai suka yi cudanya da gwamnan Nasarawa

Abba Kabir ya yi wa malaman Musulunci alkawarin inganta addini
Abba Kabir ya karbi bakuncin majalisar malaman Musulunci domin buda baki. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Asali: Facebook

Abba zai sauya filin idi zuwa Cibiyar Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi Bature DawakinTofa, daraktan yada labarai da hulda da jama’agidan gwamnati, Kano shi ya sanar da haka a shafin Facebook.

Taron ya ba da dama don karfafa hadin kai, girmama rawar da malamai ke takawa wajen samar da zaman lafiya, tare da bayyana muhimman ayyukan raya harkokin addini.

A yayin taron, Gwamna Yusuf ya sanar da shirin sauya filin Idi na Kofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa domin harkokin addini, maimakon barin wurin haka bayan bukukuwa biyu kawai a shekara.

Ya jaddada cewa ko da yake ana amfani da wurin sau biyu a shekara, sauya shi zuwa Cibiyar Musulunci ta zamani zai samar da wurin yada addini da ilimi.

Yaushe za a kafa tubalin Cibiyar Musulunci?

Abba Kabir ya kara da cewa za a kafa harsashin ginin cibiyar ne makonni biyu bayan Sallar Idi, sannan a mika shi ga malaman addini domin tafiyar da ita.

Kara karanta wannan

An karrama Buhari tare da manyan malamai da 'yan siyasar Najeriya

Gwamnan ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na gyaran dukkanin masallatan Juma'a a jihar, domin su dace da matsayin da ya dace da masu ibada.

Ya umurci Kwamishinan Harkokin Addini da ya tattara sunayen masallatan da ke bukatar gyara cikin gaggawa don daukar matakin gwamnati.

Haka kuma ya bayyana cewa ana gina sabon babban masallacin Juma’a na gidan gwamnati, wanda zai dauki masu ibada da dama fiye da abin da ake da shi yanzu.

Abba Kabir ya yi wa malaman Musulunci godiya kan hada kan al'umma
Abba Kabir ya yi alkawarin gyara masallatan Juma'a a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Abba Kabir ya godewa malaman Musulunci

Gwamna Yusuf ya godewa malamai bisa addu’o’i, jagoranci da gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.

Ya bukaci su ci gaba da hada kan al'umma da raya zaman lafiya, yana jaddada hadin gwiwar gwamnati da kungiyoyin addini.

A madadin malaman addini, Sheikh Muhammad Nasir Adam, limamin masallacin Sheikh Ahmad Tijjani, ya yabawa hangen nesa na gwamnan, yana cewa addinin Musulunci yana karfafa ciyar da masu azumi da raya wuraren ibada.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Ya tabbatarwa da gwamnati cewa malamai za su ci gaba da bayar da cikakken goyon baya da addu’a don cigaban jihar Kano.

Taron buda bakin ya samu halartar mambobin Hukumar Shari’a, Majalisar Zartaswa da wasu manyan baki daga sassa daban-daban na jihar.

Ramadan: Abba Kabir ya fara ciyar da Musulmai

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyar da masu karamin karfi kullum yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Mataimakin gwamna, Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya kaddamar da ciyarwar a ranar Litinin 3 ga watan Maris, 2025 inda ya ce mutum 91,000 za su amfana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng