SDP: An Zargi Gwamnan APC da Neman Marin Shugaban Jam'iyyar El Rufa'i
- Jam’iyyar SDP ta zargi Gwamna Inuwa Yahaya da yunkurin kai wa shugabanta mari a filin jirgin sama
- Sai dai gwamnatin jihar Gombe ta musanta zargin, tana mai cewa babu wani rikici da ya faru tsakninsu
- Duk da haka, jam'iyyar SDP ta ce babu wata barazana da za ta hana ta ci gaba da fafutukar siyasa a jihar Gombe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jiahr Gombe – Rahotanni na nuni da cewa rikici na neman barke wa tsakanin jam'iyyar SDP da gwamnatin jihar Gombe.
Hakan na zuwa ne bayan SDP ta zargi gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, da yunkurin zagba wa shugabanta, Comrade Modibbo, mari a filin jirgin sama.

Asali: Facebook
Sai dai kakakin gwamnatin jihar ya bayyana zargi a matsayin ƙarya da rashin tushe a wani sako da ya wallafa a Facebook, yana mai cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SDP ta ce ana yi mata barazana a Gombe
A wata sanarwa da jam’iyyar SDP ta fitar, ta bayyana cewa tana fuskantar barazana daga gwamnatin jihar bayan ta fara aiwatar da ayyuka a Gombe.
Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar a jihar, Kwamared Modibbo, ya ce:
"Babu wata barazana da za ta hana SDP cimma burinta. Muna fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya ta gaskiya kuma ba za mu yarda a takura mana ba."
Shugaban jam’iyyar ya bukaci magoya bayansu su kasance a faɗake a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Gwamnatin Gombe ta mayar da martani
Sai dai a martaninta, gwamnatin Gombe ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa ba gaskiya ba ne.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya ce:
"Babu wani rikici da ya faru a filin jirgin sama. Wannan ƙarya ce tsagwaron ta da ake ƙoƙarin amfani da ita don jan hankalin jama'a."

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa
Misilli ya ce SDP tana ƙoƙarin yin farfaganda mara tushe don tada hankalin jama’a, ya bukaci jam’iyyar da ta tsaya tsayin daka wajen yin siyasar da za ta amfani al’umma.
"Gombe na bukatar siyasar da za ta kawo ci gaba, ba irin wannan tarzoma da ƙirƙira labaran ƙarya ba,"
-Ismaila Uba Misilli
Har yanzu SDP ba ta yi martani ba
A halin yanzu, ana jiran jin matakin da SDP za ta ɗauka a kan martanin da gwamnatin jihar ta yi, yayin da siyasar Gombe ke ƙara ɗaukar sabon salo.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya sanar da ficewa daga jam'iyyar APC zuwa SDP a ranar Litinin.

Asali: Twitter
El-Rufa'i zai hada kan 'yan adawa
A wani rahoton, kunji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya fara kiran 'yan adawa su hada kai domin kwace mulki a hannun APC.
El-Rufa'i ya bayyana haka ne bayan komawa jam'iyyar adawa ta SDP saboda a cewarsa, APC ta kauce daga turbar asali da aka gina ta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng