Kotu Ta Dauki Mataki a Shari'ar Neman Hana Jonathan Tsayawa Takara a 2027

Kotu Ta Dauki Mataki a Shari'ar Neman Hana Jonathan Tsayawa Takara a 2027

  • Ana ci gaba da sauraron karar da ke kalubalantar cancantar Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027
  • Lauyan wanda ake kara ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar wadda ta shafi tsohon shugaban kasar na Najeriya
  • Alkalin kotun ya dauki mataki bayan an nemi wanda ya shigar da karar da lauyansa yayin zaman da aka gudanar

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai shari'a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ɗage sauraren ƙarar da aka shigar kan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Alkalin ya dage karar ne wadda ke ƙalubalantar cancantar Goodluck Jonathan na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, sakamakon rashin halartar mai shigar da ƙarar da lauyansa a kotu.

Kotu ta dage shari'ar Jonathan
Tsohon sbugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce mai shari'a Peter Lifu ya sanya ranar 15 ga Mayu, 2026, a matsayin ranar zama na gaba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya san makomarsa da NDC ta yi matsaya kan tikitin takara

Mai shari'ar ya yi gargaɗin cewa za a iya cin tarar mai shigar da karar idan har ya sake rashin halartar zaman kotu.

Mai shigar da kara bai halarci kotu ba

Yayin zaman kotun, lauyan wanda ake ƙara, Chris Uche (SAN), ya ja hankalin kotun kan rashin halartar mai ƙarar, inda ya bayyana cewa a baya ma an ɗage maganar ne bisa buƙatar mai ƙarar.

Daga baya, kotun ta tambayi magatakardan kotu ko an samu wata takarda da ke bayyana dalilin rashin halartar mai ƙarar. Magatakardan ya amsa da cewa babu wata wasiƙa makamanciyar haka a gaban kotun.

Haka kuma, an samu saɓani game da isar da takardar sanarwar zama ga sauran ɓangarorin, inda aka bayyana cewa ba a isar wa hukumar INEC da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) takardun ba, sabanin umarnin da kotun ta bayar tun farko a ranar 8 ga watan Mayu.

Lauyan Jonathan na so a yi watsi da karar

Lauyan wanda ake ƙara ya dage kan buƙatarsa ta a yi watsi da ƙarar, yana mai kawo hujjar cewa kotu tana da ikon yin watsi da ƙarar, jaridar gazettngr ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Yaron Atiku Abubakar ya sayi fam a ADC, zai nemi takarar sanata a Adamawa

Ya ƙara da cewa mai shigar da ƙarar yana da alhakin tabbatar da cewa an isar da dukkan takardun kotu da sanarwar zama yadda ya kamata, musamman a magana mai muhimmanci ga jama’a da ta shafi cancantar tsohon shugaban ƙasa na neman muƙami.

A cewarsa, bayanan da ke cikin fayil ɗin kotun sun nuna cewa ba a isar wa INEC da AGF takardun yadda ya kamata ba, sannan ba su shigar da wani martani kan ƙarar ba.

Ana shari'a da Jonathan a gaban kotu
Goodluck Jonathan na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Ana so kotu ta ci tara

Uche ya kuma buƙaci kotun da ta ci tarar mai ƙarar saboda rashin halartar zaman kotu ba tare da wani bayani ba.

Sai dai, kotun ta zaɓi bai wa mai shigar da ƙarar wata damar, inda ta ɗage shari'ar zuwa ranar 15 ga Mayu, 2026, tare da bayar da umarnin cewa dole ne a isar wa dukkan ɓangarorin takardun sanarwa kafin zama na gaba.

Jonathan zai sake fitowa takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa,Goodluck Jonathan, ya amsa kiran 'yan Najeriya kan sake fitowa takara a zaben 2027.

Wani babban jami'i a tawagar Jonathan ya tabbatar da hakan, inda ya ce an dauki wannan matakin ne bayan doguwar tattaunawa

Babban burin tsohon shugaban kasar shi ne ya lallashi yan Najeriya su sake ba shi dama domin ya farfado da tattalin arzikin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng