Sauyin da Za a Iya Gani a SDP bayan Komawar El Rufai Jam'iyyar
FCT, Abuja - Jam'iyyar SDP mai adawa a Najeriya ta samu ƙaruwa bayan komawar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, zuwa cikinta.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya koma jam'iyyar ne bayan ya sanar da ficewarsa daga APC a ranar Litinin, 10 ga watan Maris 2025.

Asali: Twitter
Tarihin jam'iyyar SDP a siyasar Najeriya
Jam'iyyar SDP an kafa ta ne a shekarar 1989 a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida, cewar rahoton jaridar Thisday.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar tana ɗaya daga cikin jam'iyyu biyu da suka fafata a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993.
Mafi yawancin shugabannin jam'iyyar a wancan lokacin ƴan Arewa ne, inda aka zaɓi Babagana Kingibe a matsayin shugaba a shekarar 1990, wanda ya yi nasara a kan abokin takararsa Mohammed Arzika.
A wancan lokacin gwamnatin tarayya ce ke samar da mafi yawan kuɗin da jam'iyyar ke amfani da su, sai wasu tsirarun mutane da suka haɗa da Shehu Musa Ƴar'adua, MKO Abiola da Francis Nzeribe.
Manyan jiga-jigan jam'iyyar a wancan lokacin sun haɗa da Atiku Abubakar, Jerry Gana, Abubakar Rimi, Rabiu Musa Kwankwaso, Umaru Yar’ Adua, Abdullahi Aliyu Sumaila, Dapo Sarumi, Sule Lamido, Magaji Abdullahi.
Sauran sun haɗa da Tony Anenih, Lamidi Adedibu, Albert Legogie, Iyorchia Ayu, Fidelis Tapgun, Moses Adasu, Boss Mustapha, Bola Tinubu da sauransu.
Tasirin SDP a siyasar Najeriya
Jam'iyyar SDP ta taka muhimmiyar rawa a siyasar a jamhuriya ta huɗu, ta fafata a zaɓukan majalisar dattawa da majalisar wakilai da aka gudanar a shekarar 1992.
SDP ta lashe kaso 57% na kujerun majalisar dattawa da kaso 53% na kujerun majalisar wakilai a zaɓen na shekarar 1992.
Jam'iyyar SDP ta fafata a zaɓen shugaban ƙasa da aka soke na shekarar 1993, wanda ake hasashen ɗan takararta, Moshood Abiola, ya lashe.
Sai dai, tun daga wannan lokacin, tasirin SDP ya yi baya a siyasar Najeriya, inda manyan jiga-jiganta suka fice suka samar da wasu jam'iyyun.

Kara karanta wannan
"Mai jiran gado": Martanin 'yan Najeriya bayan El Rufai ya fice daga APC zuwa SDP
A shekarar 2023, SDP ta shiga zaɓen shugaban ƙasa, inda Adewole Adebayo ya yi takara a ƙarƙashinta.
Sai dai, jam'iyyar ba ta taɓuka wani abin a zo a gani ba a zaɓen shugaban ƙasan wanda Bola Tinubu na APC ya lashe.
Wane matsayi SDP take ciki a yanzu?
A halin yanzu jam'iyyar SDP tana daga cikin jam'iyyun adawan da suke motsawa a siyasar Najeriya.
Jam'iyyar ta lashe kujerun sanata guda biyu a jihar Nasarawa a zaɓen 2023, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Wace rawa El-Rufai zai taka a SDP?
Wasu na ganin komawar Nasir El-Rufai zuwa jam'iyyar SDP ba ta rasa nasaba da burinsa na yin takarar shugaban ƙasa.
Komawar El-Rufai zuwa SDP zai zama babban tagomashi a gare ta duba da irin sunan da ya yi da magoya bayan da yake da su a siyasar Najeriya.
Ana hasashen cewa komawar El-Rufai zuwa SDP zai buɗe ƙofar da wasu manyan ƴan siyasa za su sauya sheƙa zuwa cikinta.
Bayan nan kuma ya sha alwashin hada-kai da jagororin hamayya domin ganin an kawo karshen gwamnatin APC a 2027.
SDP da siyasar Kaduna a 2027
A kwanakin baya ne aka zaɓi Nasiru Abdullahi Mai Kano wanda makusancin Nasir El-Rufai ne a matsayin shugaban jam'iyyar SDP a Kaduna, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Jam'iyyar SDP za ta iya sauya akalar siyasar jihar Kaduna a zaɓen 2027, duba da irin magoya bayan da Nasir El-Rufai yake da su a jihar.
Ana hasashen cewa jam'iyyar za ta taka muhimmiyar rawa a zaɓukan ƴan majalisu da gwamna a Kaduna a shekarar 2027.
A halin yanzu mutanen El-Rufai irinsu Hafsat Muhammad Baba da Ja'afar Ibrahim Sani sun yi sallama da APC zuwa SDP.
APC ta yi martani kan ficewar El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta fito ta yi magana kan ficewar da Nasir El-Rufai ya yi daga cikinta zuwa SDP.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta damu da ficewar da tsohon gwamnan ya yi ba.
APC ta bayyana cewa ficewar El-Rufai ba abin da zai dame ta ba ne, domin ta maida hankali ne kan nasarar Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a zaɓen 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng