Kishin-kishin: Bafarawa na shirin ficewa daga PDP ya koma APC

Kishin-kishin: Bafarawa na shirin ficewa daga PDP ya koma APC

- Bafarawa na shirin ficewa daga PDP ya koma APC

- An ga hoton shi tare da Tinubu da Wamakko

- Daman dai can da shi aka kafa APC din a shekarar 2014

Wani hoto da aka dauka da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa da Sanata Alu Magatakarda Wamakko da kuma jigo a jam'iyyar APC ta kasa, Cif Bola Tinubu ya haifar da rudani a dandalin sadarwar zamani.

Kishin-kishin: Bafarawa na shirin ficewa daga PDP ya koma APC

Kishin-kishin: Bafarawa na shirin ficewa daga PDP ya koma APC
Source: Facebook

KU KARANTA: Fayose ya mika takardar barin gwamnatin sa

Ganin mutanen 3 ne dai ya sanya aka fara kishin-kishin din cewa tsohon gwamnan na jihar ta Sokoto Attahiru Bafarawa na shirin fita daga jam'iyyar sa ta PDP zuwa jam'iyyar APC ne.

Idan dai mai karatu bai manta ba Attahiru Bafarawa na cikin wadanda aka kafa jam'iyyar APC da su amma suka fita bayan dawowar gwamnonin jam'iyyar PDP a shekarar 2014.

Haka zalika dai shi tsohon gwamnan Bafarawa ya nemi tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2019 inda bai yi nasara ba a satin da ya gabata.

A wani labarin kuma, Bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya ya yafewa Atiku Abubakar tare da goya masa baya a kan takarar da yake yi ta shugaban kasa a 2019, wasu manyan janar-janar har biyu suma sun nuna goyon bayan su gareshi.

Manyan tsaffin jami'an sojin dai su ne Manjo Janar David Jemibewon da kuma Birgediya Janar Ajibola Togun wadanda kuma dukkan su sun rike manyan mukamai a lokutan baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel