Bafarawa: Koda na fadi zaben fidda gwani bazan bar PDP ba
Bafarawa yace ko da zai sha kasa a zaben fidda gwani da za ayi na neman tikitin takarar shugaban kasa, bai ga dalili da zai saka ya bar jam'iyyar PDP ba
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, sannan kuma daya daga cikin masu neman tikitin kujerar shugabancin kasar nan karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, yace ba zai bar jam'iyyar ba koda ya sha kaye a zaben fidda gwani.
"Ina nan daram a PDP koda ba ni aka tsayar a neman shugabancin kasar ba, ra'ayin al'umma ne farko. A kowacce gasa akwai mai nasara da kuma wanda zai fadi," Bafarawa yace hakan a ranar Litinin a garin Minna.
DUBA WANNAN: Wani bala'i da ya taso a kasar Amurka, da har yanzu an kasa shawo kanshi
Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa a taron delegate na jam'iyyar PDP da akayi domin shirin taron kasa na jam'iyyar PDP da za'ayi a 5-6 ga watan Octoba, Bafarawa ya fadi hakan.
"Akwai mutanen da suka shigo jam'iyyar don su samu damar hayewa kujerar gwamna ko shugaban kasa, wanda a ganina son kai ne kawai. Ko na samu an tsayar dani ko ba a tsayar dani ba, zan zauna a jam'iyyar tare da tabbatar da nasarar wanda aka tsayar," inji shi.
Ya bukaci yayan jam'iyyar da su hada kai, gani da cewa hadin kai ne kawai zai sa su kayar da Gwamnatin APC kuma su daukaka Najeriya.
Bafarawa ya kwabi yan Najeriya da suke neman kujerun siyasa da kada su ga hakan a matsayin ko a mutu, ko a rayu. Gyara kasar ya zamo shine jigon su.
Ya bukaci delegate din dasu zabe shi a zaben fidda gwani da ke zuwa kuma yayi alkawarin tabbatar da dokoki da chanji da zasu kawo gyara a Najeriya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng