'Gwamnonin Arewa Wawaye ne': Sowore Ya Yi Kakkausar Suka kan Rufe Makarantu a Ramadan

'Gwamnonin Arewa Wawaye ne': Sowore Ya Yi Kakkausar Suka kan Rufe Makarantu a Ramadan

  • Omoyele Sowore ya soki gwamnonin Arewa kan rufe makarantu yayin Ramadan, yana mai cewa hakan jahilci ne kuma wawanci ne
  • Ya ce ko Saudiyya ba sa rufe makarantu saboda azumi, yana cewa shugabannin Najeriya sun jahilci addini kuma ba su fahimci ilimi ba
  • Sowore ya bukaci gwamnati ta rufe ofisoshin gwamnati maimakon makarantu, yana mai cewa azumi lokaci ne da ake so yara su yi karatu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya yi kakkausar suka ga gwamnonin Arewa kan rufe makarantu yayin azumin Ramadan.

Sowore ya bayyana matakin na gwamnonin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi a matsayin “jahilci” da “wawanci” yana mai cewa addini bai kamata ya hana ilimi ba.

Sowore ya yiwa gwamnonin Arewa martani kan rufe makarantu a Ramadan
Sowore ya kira gwamnonin Arewa da 'wawaye' saboda sun rufe makarantu a lokacin Ramadan. Hoto: @YeleSowore, @SenBalaMohammed, @dikko_radda
Asali: Twitter

'Gwamnonin Arewa jahilai ne' - Sowore

Kara karanta wannan

Dalibai sun fusata kan rufe makarantu a Arewa, NANS ta shirya zanga-zanga

A wata hira da SaharaReporters ta wallafa, Sowore ya tambayi dalilin da yasa Najeriya ke barin addini ya shafi tsarin ilimi a kasar da ke kan tsarin dimokradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ko a Saudiyya, inda Musulmi ke tafiya don Umrah, ba sa rufe makarantu yayin Ramadan, yana mai cewa shugabannin Najeriya sun jahilce addini.

“Saudiyya, inda mutane ke tafiya Umrah—sun rufe makarantu? Wadannan mutanen (gwamnonin Arewa) jahilai ne kawai. A takaice, zan ce wawaye ne,” in ji Sowore.

Ya kara da cewa idan ya zama shugaban kasa, ba za a bar jihohi su yi amfani da addini wajen tafiyar da mulki ba.

'A raba addini da gwamnati - Sowore

Mai rajin kare hakkin bil Adamar ya ce:

“Ina a matsayin shugaban kasa, babu wata jiha da za ta rufe makarantu saboda azumi. Wannan abu ya zama ruwan dare a Najeriya."

Ya kuma ce hatta makarantun Islamiya suna tafiya hutu, yana mai tambayar ta yadda dalibai za su koyi Al-Qur’ani idan an hana su zuwa makaranta?

Kara karanta wannan

Ramadan: CAN za ta yi shari'a da jihohin da suka rufe makarantu, ta kafa sharuda

Sowore ya soki shugabannin da ke rufe makarantu, yana mai cewa a Saudiyya ba sa yin hakan domin suna bukatar malamai masu ilimin Qur’ani.

Ya jaddada cewa matsalar addini ba ta takaita ga Arewa kadai ba, kuma ya shaida cewa rabe aya da tsakuwa tsakanin addini da gwamnati zai fi amfani ga kasa.

Sowore ya ce:

“Shi ya sa Karl Marx ya ce addini 'ruwan wankin kwakwalwa' ne ga talakawa; da zarar sun sha, sai su manta da komai. Don haka dole a ware addini da gwamnati.”

Sowore ya ce malamai za su yi fatawa a kansa

Sowore ya yi kakkausar suka ga gwamnonin Arewa kan rufe makarantu a Ramadan
Sowore ya ce malamai za su fara yin fatawa kan kalamansa saboda rashin son gaskiya. Hoto: @YeleSowore
Asali: Getty Images

Ya bukaci a rufe ofisoshin gwamnati maimakon makarantu, yana mai cewa za a fi amfani da kudin wajen ilmantar da yara.

Sowore ya ce rufe makarantu bai da amfani, domin kimiyya ta tabbatar cewa yayin azumi, kwakwalwa na aiki da kyau fiye da lokutan da ba a azumin.

Ya kara da cewa akwai malaman addini da ba sa son ana fada masu gaskiya, yana mai cewa za su iya fitowa da fatwa a kansa don sukar kalamansa.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

Sowore ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ake samun cece-kuce kan matakin rufe makarantu, wanda ya jawo CAN ta ce za ta yi shari'ar da gwamnonin.

Kalli bidiyon Swore a nan kasa:

Gwamnan Bauchi ya rufe makarantu a Ramadan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Sanata Bala Mohammed ta rufe dukkanin makarantun jihar saboda azumin Ramadan.

Gwamnatin ta rufe makarantun firamare har zuwa na gaba da sakandare, yayin da aka ce hutun na cikin jadawalin karatun 2024-2025 na jihar da tuni aka amince da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.