Zargin Lalata: Akpabio Ya Tono Abin da Ya Faru a Daren Auren Sanata Natasha

Zargin Lalata: Akpabio Ya Tono Abin da Ya Faru a Daren Auren Sanata Natasha

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya tuna baya kan alaƙar da ke tsakaninsa da mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Godswill Akpabio ya bayyana cewa Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan abokinsa ne, domin ya halarci bikin aurensa da Natasha a jihar Kogi
  • Shugaban majalisar dattawan ya tuna da cewa har kwana ya yi a masana'antar simintin Dangote da ke Obajana a Kogi a ranar auren nasu
  • Godswill Akpabio ya yi waɗannan bayanan ne a zaman majalisar na ranar Alhamis inda aka tattauna kan zargin da ake yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan taƙaddamarsa da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Godswill Akpabio ya bayyana cewa ya kwana a masana'antar simintin Dangote da ke Obajana, jihar Kogi, a ranar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi aure.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Sanata ya yi fallasa kan rigimar Akpabio da Natasha

Akpabio ya kare kansa kan zargin cin zarafin Natasha
Akpabio ya ce yaje daurin auren Sanata Natasha Akpoti a Kogi Hoto: Natasha H Akpoti, Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, 6 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene alaƙar Akpabio da mijin Natasha

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa mijin Sanata Natasha abokinsa ne na ƙud da ƙud.

Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya faɗi haka ne domin nuna kusancinsa da Sanata Natasha da mijinta, a yayin da take zarginsa da ci mata zarafi.

Ya ce ya kwana a cikin masana'antar ne saboda fitilun filin jirgin saman Kogi sun lalace.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan shawarwarin da kwamitin ladabtarwa, ɗa'a da ƙorafe-ƙorafe na majalisar ya bayar.

"Na kwana a masana'antar simintin Dangote da ke Obajana, jihar Kogi, a daren bikin auren Sanata Natasha, saboda fitilun filin jirgin saman Kogi ba su da kyau."

- Sanata Godswill Akpabio

An ba majalisa shawarwari kan Natasha

Kara karanta wannan

Yadda majalisar dattawa ta yi biris da rokon Sanata kan dakatar da Natasha

Kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa ya bayar da shawarar dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida.

Haka nan, kwamitin ya buƙaci cewa dole ne Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ba majalisar dattawa hakuri saboda cin mutuncin majalisar.

A lokacin dakatarwar, kwamitin ya bayyana cewa za a cire albashinta da kuma jami’an tsaron da ke kula da ita.

Haka kuma, kwamitin ya ba da shawarar cewa bai kamata a ga Sanata Natasha a kusa da majalisar ba a tsawon lokacin dakatarwar.

Bayan wannan shawarwari, majalisar dattawa ta amince da matsayar kwamitin, inda shugaban majalisar ya sanar da dakatar da ita na tsawon watanni shida.

Natasha ta sake miƙa ƙorafi kan Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa Natasha Akpoti-Uduaghan wacce ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya, ta sake miƙa ƙorafi kan Sanata Godswill Akpabio.

Sanata Natasha Akpoti ta sake shigar da ƙorafin ne a kan shugaban majalisar dattawan kan zargin da take yi masa na yunƙurin yin lalata da ita tare da ci mata zarafi.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa

Ta dai miƙa ƙorafin ne bayan majalisar ta ƙi karɓar wanda ta fara gabatarwa a gabanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng