Tsohon Jigon APC Ya Fadi Kuskuren El Rufai wajen Komawa Jam'iyyar SDP
- Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Salihu Lukman ya hango matsala a sauya sheƙar da Nasir El-Rufai ya yi
- Salihu Lukman ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kaduna ya yi saurin ficewa daga jam'iyyar APC zuwa SDP mai alamar doki
- Tsohon jigon APC ya nuna kamata ya yi El-Rufai ya ƙara haƙuri har sai an kammala tattaunawar da ake yi kan haɗakar jam'iyyun adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa (Arewa maso Yamma), Dr. Salihu Lukman, ya yi magana kan sauya sheƙar Nasir El-Rufai zuwa jam'iyyar SDP.
Salihu Lukman ya bayyana sauya sheƙar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, daga APC zuwa jam’iyyar SDP a matsayin abin da ya yi cikin sauri.

Asali: Twitter
Salihu Lukman ya bayyana haka ne yayin da yake magana da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, cewar rahoton jaridar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa SDP a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
A cikin sanarwar, El-Rufai ya bayyana wasu dalilai da suka sanya shi ɗaukar matakin ficewa daga jam'iyyar APC.
Lukman ya hango matsala a sauya sheƙar El-Rufai
Salihu Lukman, wanda ya kasance abokin siyasar El-Rufai kuma tsohon mamba na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na APC, ya nuna damuwarsa kan sauya sheƙar tsohon gwamnan.
Ya nuna damuwar cewa sauya sheƙar tsohon gwamnan na iya kawo cikas ga tattaunawar da ake yi domin kafa haɗakar jam’iyyun siyasa kafin zaɓen 2027.
Ko da yake ya ce dama an yi hasashen sauya sheƙar El-Rufai, sai dai ya yi nuni da cewa ya kamata ya yi haƙuri kaɗan don ba wa tattaunawar haɗakar jam’iyyun damar kammaluwa.
“An riga an yi tsammanin hakan. Tun bayan hirar da ya yi a wani gidan talabijin na ƙasa, ana iya ganin alamar hakan. Amma ko zai yi hakan da wuri, shi ne ni kai na abin da ban sani ba."

Kara karanta wannan
2027: Yan adawa na shirin firgita Tinubu, ƙusa a PDP ya ce guguwar canji za ta tafi da APC
"Abin da na yi tsammani shi ne ya ɗan ƙara yin haƙuri don mu yi aiki tare a matsayin ƙungiya bisa tattaunawar da ake yi a halin yanzu."
- Salihu Lukman
Shin Salihu Lukman zai koma SDP?
Duk da cewa ya amince cewa El-Rufai na da ƴancin shiga kowace jam’iyyar siyasa da yake so, tsohon jigon na APC ya yi gargaɗin cewa lokacin da ya zaɓa na iya haifar da illa ga ƙoƙarin haɗakar ƴan adawa.
Da aka tambaye shi ko zai bi El-Rufai zuwa SDP, ya ce hakan zai iya yiwuwa ne idan jam’iyyar ta cika wasu sharuɗɗa, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
“A halin yanzu, ba su cika sharuɗɗan ba. Muna tattaunawa, babu shakka. Idan sun cika sharuddan gobe, to babu matsala."
- Salihu Lukman
Fadar shugaban ƙasa ta yi wa El-Rufai martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan sauyar da Nasir El-Rufai ya yi daga jam'iyyar APC zuwa SDP.
Mai ba shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne don El-Rufai ya fice daga jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng