Najeriya Ta Sake Yin Babban Rashi, Tsohon Minista Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Sake Yin Babban Rashi, Tsohon Minista Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon ƙaramin ministan harkokin waje da ya yi aiki a gwamnatin Olusegun Obasanjo, Dubem Onyia ya rasu yana da shekara 73 a duniya
  • Marigayin ya riga mu gidan gaskiya ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025 a birnin tarayya Abuja kamar yadda iyalansa suka tabbatar
  • Onyia wanda ya fito daga jihar Ogun ya ba da gudummuwa mai tarin yawa a tarihin Najeriya kuma ya riƙe muƙamai daban-daban a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Dubem Onyia, ya rasu yana da shekaru 73.

Majiyoyi daga iyalansa da abokan aikinsa sun tabbatar da rasuwarsa a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025.

Dubem Onyia.
Tsohon ministan harkokin waje, Dubem Onyia ya kwanta dama yana da shekaru 73 Hoto: @elicathage
Asali: Twitter

Rahoton The Cable ya nuna cewa Onyia, wanda ya fito daga jihar Enugu, ya ba da gudummuwa mai tarin yawa tarihin siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa, zai kara da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 1999, aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai, amma daga baya ya yi murabus domin karɓar mukamin karamin ministan harkokin waje a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Muƙaman da ya riƙe a gwamnatin Najeriya

Tun daga lokacin da ya shiga siyasa, Dubem Onyia ya taka rawa sosai kuma ya riƙe muƙamai daban-daban gwamnati.

Ya shugabanci kwamitoci da dama, kuma ya kasance mutum mai kwarewa a harkokin diflomasiyya da ci gaban tattalin arziki.

Daga cikin muhimman mukamai da ya riƙe sun haɗa da, shugaban kwamitin fasaha na hukumar kula da iyakokin Najeriya, da shugaban kwamitin hadin gwiwar tattalin arziki.

Har ila yau marigayin ya rike muƙamin shugaban kwamitin kula da iyakoki tsakanin Najeriya da Sao Tome da Principe.

Baya ga rawar da ya taka a gwamnati, Onyia ya shugabanci kamfanoni da dama kuma ya kasance mamba a kwamitoci na gwamnati da sauran hukumomi masu zaman kansu.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

Haka kuma, yana cikin amintattun gidauniyar Shehu Musa Yar’Adua, mai fafutukar kawo cigaban dimokuradiyya a Najeriya.

Taƙaitaccen tarihin tsohon ministan

An haifi Dubem Onyia a ranar 23 ga Fabrairu, 1952, a jihar Enugu. Wannan yana nufin ya bar duniya yana mai shekaru 73.

Ya fara karatun firamare a Ikeja District Primary School, Lagos, sannan ya halarci Fatima College, Ikire, da kuma College of Immaculate Conception, Enugu.

Daga nan, ya tafi ƙasar Birtaniya (UK) domin cigaba da karatu, inda ya yi digiri a Northampton College of Technology, Nene College (wanda ke da alaƙa da Leicester University), da kuma Coventry Polytechnic.

Mutuwar Dubem Onyia babban rashi ne ga Najeriya, musamman ma ga mutanen jihar Enugu, da dukan waɗanda suke da alaƙa da shi.

Abokan aikinsa da iyalansa sun bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin kasa, haziki, kuma mutum mai hangen nesa.

Tsohon mataimakin gwamna ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yi wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Patrick Adaba rasuwa a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Nasir El Rufai ya fitar da sanarwar ficewa daga APC zuwa SDP

Gwamnatin jihar Kogi, ta nuna alhini tare da tura sakon ta'aziyya bisa rasuwar Cif Adaba, tana mai bayyana shi a matsayin mutum mai dattako.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng