2023: Malamin Musulunci ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa, ya nemi tallafin kuɗi

2023: Malamin Musulunci ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa, ya nemi tallafin kuɗi

  • Wani Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Afeez Akinola na Ibadan jihar Oyo, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari a 2023
  • Shehin Malamin ya ce Najeriya na bukatar mutum mai tsoron Allah da zai iya shawo kan matsalolin da suka baibayeta
  • Ya roki dattawan ƙasar nan su taimaka masa da goyon baya, sannan mutane su tallafa masa da kuɗaɗe

Oyo - Wani Malamin Musulunci ɗan asalin Ibadan, Sheikh Abdul-Afeez Akinola, ya ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.

Tribune Online ta rahoto cewa Malamin ya tsaya takara ne ƙarƙashin inuwar APC, kuma ya ayyana niyyarsa ranar Talata.

Ya ce da zaran yan Najeriya sun masa ruwan kuri'u ya ɗare madafun iko, zai fara kawar da talauci, matsalar tsaro da rashin adalcin da ake fama da shi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ngige ya ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2023, ya faɗi wasu kalamai kan Buhari da APC

Sheiƙmkh Afeez Akinola na Ibadan.
2023: Babban Malamin Musulunci ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa, ya nemi tallafin kuɗi Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Malamin ya roki tsaffin shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida, Janar Abdsalam Abubakar da sauran dattawan ƙasa su taimaka masa ya cika burinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a gaban taron magoya bayansa a Ibadan jihar Oyo, Malamin ya ce Najeriya ta wayi gari cikin wani yanayi abun takaici kuma Allah ya turo shi ya zama waraka ga matsalolin ƙasa.

Abun da nake bukata domin cika burina - Sheikh Azeez

Malam Azeez ya jaddada cewa Najeriya na bukatar a sake gina ta tare da canza rayuwar talakawa da masu karamin karfi.

The Nation ta rahoto A kalamansa ya ce:

"Ina bukatar tallafin kuɗi daga hannun mutane domin gyara Najeriya har mu wayi gari ta zama yadda kowa zai alfahari da ita."
"Sama da kashi 80% na yan Najeriya Talakawa ne, sabida haka shugaban ƙasa mai tsoron Allah da kuma aiki tuƙuru wajen kawo cigaba ake bukata a 2023."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

Bayan haka, ya sha alwashin cewa idan ya zama shugaban ƙasa za'a samu ingantaccen tsaro, cigaban tattalin arziki, wutar lantraki da ruwan sha.

A wani labarin kuma Kwamishinoni uku da hadiman gwamna mai ci sun sauya sheka zuwa PDP a jiha ɗaya

Guguwar sauya sheƙa ta shiga cikin majalisar kwamishinoni da sauran hadiman gwamnatin jam'iyyar PDP a jihar Oyo.

Kwamishinoni uku da wasu hadiman gwamna Seyi Makinde sun sauya sheka daga ADC zuwa PDP mai mulkin jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel