Faransa Ta Fara Zartar da Yarjeniyar da Ta Yi da Tinubu a Najeriya
- Gwamnatin Faransa ta tabbatar wa NDLEA tallafin horaswa, karin kwarewa da kayan aiki domin yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi
- Laftanal Janar Regis Colcombet ya ce tattaunawar na daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin shugaba Macron da shugaba Tinubu
- Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (Mai ritaya) ya bukaci karin horo kan dabarun aiki, binciken intanet da kuma fasahar zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Faransa ta tabbatar wa Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun yoyi (NDLEA) karin tallafi a fannin horaswa, inganta kwarewa da samar da kayan aiki.
An ruwaito cewa matakin na daga cikin kokarin da ake yi na dakile yaduwar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Asali: Twitter
Hukumar NDLEA ce ta wallafa bayanai kan yadda shugabanninta suka tattauna da jami'an Faransa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan ganawar Daraktan Tsaro da Hadin Gwiwar Tsaro a Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa, Laftanal Janar Regis Colcombet da Shugaban NDLEA, Buba Marwa.
Laftanal Janar Regis Colcombe da tawagarsa sun gana da NDLEA ne a hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata, 4 ga Maris, 2025.
Batun hadin gwiwar Najeriya da Faransa
Laftanal Janar Colcombet ya ce ganawar na daga cikin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a ziyarar Shugaba Bola Tinubu zuwa Faransa watanni uku da suka gabata.
Colcombet ya ce tun kusan shekaru biyu da suka gabata, sun fara tattaunawa da NDLEA kan batun hadin gwiwa.
"Abu ne mai matukar muhimmanci kasancewarmu a nan, domin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashenmu.
"Za mu ci gaba da aiki tare domin inganta wannan hadin gwiwa,"
- Laftanal Janar Colcombet
Ya kara da cewa, NDLEA za ta samu karin horo a fannoni daban-daban ciki har da dabarun aiki da tsaro na zamani.
Laftanal Janar Colcombet ya ce za a ware wasu jami’an NDLEA su halarci horo a cibiyar horaswa ta Faransa da ke Côte d'Ivoire.
Baya ga haka, Faransa za ta samar da kayan aiki da za su taimaka wajen inganta ayyukan hukumar.

Asali: Twitter
Buba Marwa ya bukaci karin tallafin Faransa
A nasa jawabin, Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (Mai ritaya), ya bayyana jin dadinsa da yadda dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa ke kara karfi.
Ya ce alakar na kara karfi musamman sakamakon kyakkyawar alakar da ke tsakanin shugabannin kasashen biyu.
Marwa ya gode wa Gwamnatin Faransa bisa irin tallafin da take bai wa NDLEA, sannan ya bukaci karin horo ga jami’an hukumar a fannin dabarun aiki, binciken intanet da fasahar zamani.
Daga cikin abubuwan da Buba Marwa ya bukaci karin taimako daga Faransa har da bincike kan kudin kirifto.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka
Daga cikin tawagar Faransa da suka halarci taron har da Laftanal Kanal Pierre Yves Dupe, Philippe Baurreau, Kanal Oliver Ductet, da Philippe Crespo.
An kona jami'in NDLEA a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa wasu fusatattun matasa sun kona wani jami'in hukumar NDLEA a jihar Kaduna.
Rahoton Legit ya nuna cewa matasan sun fusata ne sakamakon wani hadari da ya faru wanda hakan ya sanya suka dauki matakin kona jami'in.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng