Rikicin Siyasar Kaduna: El Rufa'i Ya Nuna Yatsa ga Uba Sani kan Tinubu
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce babu wata matsala tsakanin sa da tsohon gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i
- Uba Sani ya bayyana cewa siyasar da wasu ke yi na ƙoƙarin kafar ungulu ga gwamnatin Bola Tinubu ba ta da tushe balle makama
- Sai dai tsohon gwamna, Nasir El-Rufa’i ya yi kalamai da suke nuna cewa akwai wata matsala tsakaninsa da Uba Sani
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa akwai sabani tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufa’i.
A cewar gwamna Uba Sani, dangantakarsu tana nan lafiya ƙalau kuma babu wata matsala da ta shiga tsakaninsu.

Asali: Twitter
Legit ta gano cewa gwamna Uba Sani ya fadi haka ne a cikin wata hira da tashar talabijin ta TVC ta yi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, Uba Sani ya yi tsokaci kan ƙoƙarin da wasu ‘yan siyasa ke yi na kafa kawancen adawa domin taruwa ga gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana cewa waɗanda ke yin hakan ba don suna da wata mafita ba ne, illa kawai don neman dawo da mulki hannunsu.
'Ba na rikici da El-Rufa’i' - Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya bayyana a cikin wata hira cewa dangantakarsa da tsohon gwamna El-Rufa’i tana nan garau.
Uba Sani ya ce rashin jituwa tsakanina da Malam Nasir El-Rufa’i. Ya ce suna da kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna.
A karkashin haka ne Uba Sani ya bukaci 'yar jaridar da ke hira da shi ta mayar da hankali kan muhimman abubuwa da suka shafi Kaduna maimakon magana kan El-Rufa'i.
Maganar hadakar 'yan adawa
A kan batun siyasar kawancen da wasu ke yi don kalubalantar gwamnatin Bola Tinubu, Uba Sani ya bayyana cewa ba su da wani dalili na gaskiya da ya sa suke wannan ƙoƙari.

Kara karanta wannan
"Ka hakura da siyasa," Jama'a sun fara tsoma baki a kan rikicin El Rufa'I da Uba Sani
“Wadannan ‘yan siyasa da ke son yin kawance ba don suna da wata mafita ba ne. Suna kawai neman mulki ne
"Su ne suka mara wa Tinubu baya a zaben da ya gabata saboda sun yarda cewa shi ne mutum mafi cancanta wajen jagorantar Najeriya,”
- Uba Sani
Gwamnan ya tambayi abin da waɗannan ‘yan siyasa suka yi a lokacin da suke rike da mulki:
“Me suka yi lokacin da suke kan mulki? Me suka ƙara wa dimokuraɗiyya? Ba wanda ya kai abin da Bola Tinubu ya yi.
‘Yan Najeriya suna da wayo, kan mage ya waye,”
Martanin Nasir El-Rufa’i ga Uba Sani
A nasa ɓangaren, tsohon gwamna Nasir El-Rufa’i, wanda ke maganar kafa kawancen siyasa da zai kalubalanci gwamnatin Tinubu, ya yi martani kan lamarin.
El-Rufa’i ya wallafa a Facebook cewa:
"Yanzu na fahimci cewa gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Kaduna sama da Naira biliyan 150 a cikin watanni 18 da suka gabata, wanda hakan ya bayyana dalilin wasu abubuwan.”
Ya kara da cewa:
Rikicin El 'Mutanen Kaduna za su yi hukunci,' El-Rufa'i ga Uba Sani kan siyasa da alakarsu
Tinubu zai kafa jami'a a Ogoni
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da jami'ar fasahar muhalli a jihar Rivers.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jami'ar fasaha da za a kafa a Ogoni za ta taimaka wajen bunkasa ilimi da samar da ayyukan yi a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng