Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sabuwar Jami'ar Fasaha a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sabuwar Jami'ar Fasaha a Najeriya

  • Rahotanni na nuni da cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa Jami’ar Fasahar Muhalli ta Tarayya a Ogoni
  • An bayyana cewa wannan mataki na cikin shirin gwamnatin Tinubu na inganta ci gaban ilimi a yankunan da ba su da isassun cibiyoyin karatu
  • Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman, Daniel Bwala ya yi karin haske ga manema labarai kan amincewa da kafa jami'ar da Tinubu ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa Jami’ar Fasahar Muhalli ta Tarayya da za a yi a Ogoni, jihar Rivers.

Shugaban ya sanya hannu kan dokar ne a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin, a daidai lokacin da ministoci da mambobin majalisar zartarwa ke jiran zuwansa domin tattaunawa.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Tinubu ta nuna halinta a kan babban zabe mai zuwa," Atiku

Shugaba Tinubu
Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa jami'ar Ogoni. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanan amincewa da kafa jami'ar ne a cikin wani sako da hadimin shugaban kasar kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel Bwala ya jaddada cewa wannan matakin wani bangare ne na shirin gwamnatin Bola Tinubu na bunkasa ilimi.

Dalilan kafa jami’ar tarayya a Ogoni

Leadership ta wallafa cewa Daniel Bwala ya ce kafa jami’ar wani bangare ne na kokarin gwamnatin Bola Tinubu na tabbatar da daidaito da ci gaba a kowane yankin Najeriya.

“Idan ba ku manta ba, shugaban ƙasa ya amince da kafa wata jami’ar tarayya a yankin Kudancin Kaduna a kwanakin baya.
"Shugaban kasar ya yi haka ne don tabbatar da ingantaccen ci gaba a yankunan da ba su da isassun cibiyoyin ilimi,”

- Daniel Bwala

Ya kara da cewa kafa jami’ar zai taimaka wajen cike gibin da aka dade ana fuskanta wajen samar da cibiyoyin ilimi a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Kishin kasa da daidaito a fannin ilimi

Bwala ya bayyana cewa matakin Tinubu na nuna cewa yana da kyakkyawan hangen nesa game da ci gaban ƙasa da kuma kishin inganta ilimi a dukkan sassan Najeriya.

“Ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, babu kananan kabilu a Najeriya. Duk al’umma daya ne, kuma dukkan sassan ƙasar na da muhimmanci wajen gina ci gaban ƙasa,”

- Daniel Bwala

Ya kara da cewa shugaban ƙasar yana ganin Najeriya a matsayin kasa guda, inda bambancin harshe da kabila ba zai hana haɗin kai da ci gaba ba.

Tabbatar da haɗin kai da cigaba

Ana ganin cewa kafa Jami’ar Fasahar Muhalli a Ogoni za ta taimaka wajen tabbatar da cewa yankin yana da dama irin ta sauran yankuna wajen samun ilimi mai inganci.

Bwala ya yi nuni da cewa shugaba Tinubu na da burin ganin kowane yanki na Najeriya yana amfana da manufofin gwamnati, ba tare da nuna wariya ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

Ana sa ran cewa jami'ar ba kawai za ta taimaka wajen koyar da ilimi ba ne, har ma zata samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin yankin.

Izala ta gayyaci Bola Tinubu taro a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala mai hedkwata a Filato ta gayyaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu taron da ta shirya a Abuja.

Bayan Bola Tinubu, Izala ta gayyaci wasu manyan kasa ciki har da Atiku Abubakar domin kaddamar da gidauniyar neman taimakon N1.5bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng