"Ka Hakura da Siyasa," Jama'a Sun Fara Tsoma Baki a kan Rikicin El Rufa'i da Uba Sani
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa sai yanzu ya gane dalilin da ya sa gwamna Uba Sani ke kare Bola Tinubu
- Ya yi zargin cewa hakan ba ya rasa nasaba da tallafin kudade da suka haura Naira biliyan 150 da gwamnatin tarayya ta bai wa Kaduna
- Martanin El-Rufa’i ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa ba shi da hurumin ya tsoma baki a kan sha'anin gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Martanin tsohon gwamna, Nasir El Rufa'i ga gwamnan Kaduna, Uba Sani ya jawo ce-ce-ku-ce, aka samu rarrabuwar kai a tsakanin masu tofa albarkacin bakinsu.
Nasir El Rufa'i ya fusata da wata hira da gwamna Uba Sani ya yi, inda ya karyata cewa akwai wata matsala a tsakaninsa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
'Ba ni da hannu a ciki, Tsohon gwamna ya musanta zargin kisan tsohon minista a Najeriya

Asali: Facebook
A martanin wasu daga cikin masu bin shafukan sada zumunta, a karkashin maganar El Rufa'i a shafinsa na X, su na ganin ya dace tsohon gwamnan ya zubar da makamansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai a gefe guda, wasu na zargin gwamna Uba Sani da cin amanar tsohon ubangidansa, fiye da yadda aka saba gani a siyasar Najeriya.
Ana magana bayan El Rufa'i ya tabo Uba Sani
Tsohon gwamna, Nasir El Rufa'i ya bayyana cewa sai yanzu ya fahimci dalilan da su ka sa gwamna Uba Sani ya ke tsananin goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu.
El Rufa'i ya yi zargin cewa:
"Kullum ina kallon yadda gwamnan Kaduna ke bayyana kansa cikin irin maganganun da ke nuna son zuciya da neman faranta wa gwamnati rai.
"A da, sai na rika tambayar kaina, “Me yasa yake haka?” Sai dai, bayan tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin kudi da suka haura Naira biliyan 150 ga jihar Kaduna a cikin watanni 18 da suka gabata, yanzu komai ya bayyana a sarari."
An samu masu goyon bayan Uba Sani
Wasu daga cikin masu amfani da shafin X sun caccaki tsohon gwamna, Nasir El Rufa'i, inda ake zarge shi da take hakkin jamaa'a da goyon bayan tsohon Shugaba Buhari ido a rufe.
@Maxajee ya ce:
Haka dai kake tallatawa da kare rashin kwarewar Buhari kafin ka kai shi kotu domin kare muradun BAT. Ban ga dalilin da zai sa ka zama daga cikin mutane da ke da ikon cewa Uba Sani ga wanda zai tallata ba.
@Abubakardnk ya ce:
"Kai ma ka zo ka mana bayani akan kudin da tsohon Shugaban kasa ya rika aikowa jihar Kaduna na Paris Club da Bailout.
@ahmaad_ak
Malam ga fa mulkin nan da kai tsaye se ya je Kudu ana azabtar da kai cikin shi. Na ji dadi da Allah ya sa kaima ka shiga kunci a kan wannan mulkin.
Uba Sani ya magantu a kan El Rufa'i

Kara karanta wannan
Sarki ya jefa kansa a matsala, Gwamna ya dakatar da basarake kan cin zarafin dattijo
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya musanta jita-jitar da ke cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i ko kadan.
Sai dai, a martanin da ya wallafa a shafinsa na Facebook, El-Rufa’i ya nuna rashin jin daɗinsa kan wasu kalaman da Uba Sani ya yi, yana mai zarginsa da zama dan amshin shatan Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng