Sheikh Jingir Ya Fara Gyara Hanyar Saminaka da Ta Hada Jihohin Arewa

Sheikh Jingir Ya Fara Gyara Hanyar Saminaka da Ta Hada Jihohin Arewa

  • Shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya assasa gyaran hanyar Jos zuwa Saminaka
  • Jama’a daga kowane ɓangare, ciki har da masu hannu da shuni da talakawa, sun amsa kiran taimako domin gyaran hanyar
  • An samu gudummawar kuɗi daga shugabanni da ‘yan kasuwa, tare da fatan gwamnatin tarayya za ta duba muhimmin aikin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Shugaban Majalisar Malaman Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahya Jingir, ya assasa wani babban aikin alkhairi na gyaran hanyar Jos zuwa Saminaka.

An ruwaito cewa hanyar na da matuƙar muhimmanci ga al’umma da ke tafiya tsakanin Kano, Kaduna, da sauran jihohin Arewa.

Hanyar Saminaka
Sheikh Jingir na jagorantar gyara hanyar Saminaka. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Ibrahim Maina Muhammad ya wallafa a Facebook, Sheikh Jingir ya bayyana cewa shirin ya samu tallafi daga mutane da dama.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sabuwar jami'ar fasaha a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yunƙurin malamin ya samu karɓuwa sosai daga jama’a, ciki har da masu hannu da shuni da talakawa domin gudanar da aikin.

A cewarsa, aikin wani alkhairi ne da za a yi domin sauƙaƙa wa jama’a wahalhalun hanya da suka dade suna fuskanta.

Sheikh Jingir ya gargadi shugabanni

Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana farin cikinsa ganin yadda jama’a suka karɓi wannan yunƙuri da hannu biyu biyu.

A karkashin haka ya ke roƙon Allah Ya sanya alkhairi a cikin aikin. Kuma ya yi kira ga wadanda ke da haƙƙin yin hanyar su sani cewa Allah zai tambaye su idan ba su yi ba.

Sheikh Jingir ya nuna godiyarsa ga duk wanda ya taimaka, ko da da kuɗi, ƙarfi, ko addu’a, yana mai roƙon Allah Ya saka musu da alkhairi.

Gudummawar da aka samu wajen aikin

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kaddamar da gidauniya domin neman tallafi wajen ganin an fara gyara titin.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

Daga cikin wadanda suka taimaka da kuɗi domin aikin gyaran hanyar, an samu gudummawa daga fitattun mutane kamar haka:

  • Sheikh Sani Yahaya Jingir - N1m
  • Mataimakin shugaban majalisar jihar Filato, Hon. Isa Madaki - N2m
  • Alhaji Ya’u - N500,000
  • Shugaban gudanarwa na Izala, Sheikh Nasir Abdulmuhyi - N100,000
  • Mataimakin Shugaban ‘Yan Agaji na Ƙasa, Ibrahim Shu’aibu - N50,000

Mutane da dama sun tallafawa shirin wanda hakan ke nuna yadda jama'a ke kokarin ganin an gyara hanyar saboda lalacewar da ta yi.

Haka zalika hakan ya nuna yadda al’umma suka haɗa kai wajen ganin an cimma nasarar wannan aiki mai mahimmanci.

Martanin jama’a game da aikin hanyar

Daga cikin martanin da aka samu daga jama’a, Anas Yusuf ya ce:

"Allah ya saka wa Sheikh Sani Yahya Jingir da alheri na yunƙurin gyaran hanyar Jos-Saminaka da ya kaddamar.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kama 'yan 'daɗi soyayya' da suka yi aure a wurin shakatawa a Kano

"Wannan yunƙuri abin yabo ne matuƙa. Hanyar nan ta lalace fiye da shekaru 30 ba tare da gwamnati ta waiwaye ta ba."

Sai dai Anas ya ƙara da cewa, aikin gyaran manyan hanyoyi kamar na Saminaka na buƙatar ƙarin tallafi daga gwamnati saboda yawan kuɗin da aikin ke buƙata.

Ya wallafa a Facebook cewa:

"Da Sheikh zai yi amfani da alaƙarsa da shugaba Bola Tinubu domin sanar da shi game da lalacewar hanyar da muhimmancin gyaranta, hakan zai fi ƙarfafa wannan gidauniya."

Jama’a da dama sun yaba da wannan yunƙuri na Sheikh Jingir, suna fatan gwamnatin tarayya da ta jiha za su saka hannu a aikin.

Aikin gyaran hanyar ya zama abin koyi ga sauran shugabanni da masu hali, inda ake fatan za su taimaka wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar ayyukan alheiri da tallafa wa jama’a.

Sheikh Guruntum ya yi nasiha ga malamai

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta ba da mamaki a Kwara, ta fita a mota ta tattauna da dalibai

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi nasiha ga malaman addinin Musulunci a Najeriya.

Malamin ya yi kira ga malamai da su yi taka tsantsan kan kan yadda suke mu'amala da 'yan siyasa domin kaucewa rusa musu da'awa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng