'Buhari Ya Nuna Rashin Gamsuwa da Mulkin Bola Tinubu,' PDP Ta Tono Magana

'Buhari Ya Nuna Rashin Gamsuwa da Mulkin Bola Tinubu,' PDP Ta Tono Magana

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Allah ne kaɗai zai iya gyara Najeriya, wanda hakan ya ja hankalin 'yan Najeriya
  • Jam’iyyun adawa sun bayyana cewa wannar magana ta Buhari ta nuna gazawar gwamnati mai ci ta jam’iyyar APC
  • Jam'iyyar PDP ta ce kalaman Buhari tamkar zargin gazawar gwamnatin Tinubu ne da tabbatar da rashin tabbas kan shugabancin APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha rubdugu bayan ya bayyana cewa Allah ne kawai zai iya gyara Najeriya.

An ruwaito cewa ya yi maganar ne a yayin taron shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Katsina a ranar Asabar.

Buhari
'Yan adawa sun yi rubdugu ga Buhari. Hoto: Bashir Ahmed|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Punch ta rahoto cewa kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a dandalin sada zumunta, inda 'yan Najeriya da dama suka bayyana ra’ayoyinsu game da matsalolin kasar.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyun adawa kamar PDP, NNPP da LP sun yi tsokaci kan wannan batu, inda suka bayyana shi a matsayin hujjar gazawar gwamnatin APC.

NNPP ta ce Buhari ya nuna gazawar APC

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya ce kalaman Buhari sun nuna cewa gwamnatin APC ta kasa sauke nauyin da aka ɗaura mata.

Ladipo Johnson ya ce:

“Kalaman Buhari sun tabbatar da cewa gwamnati mai ci ba ta da wata hanya tabbatacciya da za ta bi wajen magance matsalolin Najeriya.
"Wannar gwamnatin ta dade tana tukin tsaye a kan harkokin mulki, kuma yanzu lokaci ya yi da za a samar da shugabannin da za su iya canja fasalin kasar nan.”

Johnson ya kara da cewa gwamnatin APC ta gaza samar da shugabanci nagari da ake bukata domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

PDP ta ce kalaman Buhari sun zargi Tinubu

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, ya bayyana cewa kalaman Buhari sun nuna zargi ne ga gwamnatin Bola Tinubu kai tsaye.

A cewar Timothy Osadolor:

“Ya kamata mu gode wa Buhari kan gaskiyar da ya bayyana, amma duk da haka dole ne mu fahimci cewa shi da kansa ya kafa tushen gazawar wannar gwamnatin.
"Wannar maganar tasa tana nuna gazawar Tinubu da rashin tabbas kan mulkinsa.”

Osadolor ya yi kira ga al’ummar Najeriya su tashi tsaye domin ceto kasar daga fadawa cikin matsaloli masu yawa.

Ya kara da cewa a halin yanzu Najeriya na bukatar shugabanni da za su iya ceto kasar daga fadawa cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

LP ta bukaci matasan Najeriya su tashi tsaye

Shugaban matasan jam’iyyar LP na ƙasa, Kennedy Ahanotu, ya ce bai mamakin kalaman Buhari, domin tun farko ya san ba zai iya ciyar da Najeriya gaba ba.

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Kennedy Ahanotu ya ce;

“Na dade ina cewa sai an bai wa matasa damar shugabanci sannan za mu iya ganin ci gaban dimokuradiyya.
"Sai an kawo sababbin jini sannan za a iya samun ci gaba mai ma’ana.”

Buhari ya ba 'yan Najeriya mamaki

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ba 'yan Najeriya mamaki yayin da ya yi kyauta da dalaloli.

Legit ta wallafa cewa 'yan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu cikin mamaki kasancewar shugaba Buhari bai saba haka a bayyane ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng