PDP Ta Samu Koma Baya, Babban Sanata Ya Shirya Komawa APC

PDP Ta Samu Koma Baya, Babban Sanata Ya Shirya Komawa APC

  • Sanata Ned Nwoko ya shirya tattara ƴan komatsansa daga jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Delta zuwa APC mai adawa
  • Ned Nwoko wanda yake wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa ya shirya barin PDP domin komawa jam'iyyar APC
  • Alamu sun nuna cewa sanatan baya shiri da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da ubangidansa Ifeanyi Okowa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Jam'iyyar APC a jihar Delta na shirin samun ƙaruwa ta sanata wanda zai bar PDP ya dawo cikinta.

Sanata Ned Nwoko, wanda ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, yana shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Ned Nwoko zai koma APC
Sanata Ned Nwoko ya shirya komawa APC Hoto: Ned Nwoko
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa sanatan ya tabbatar mata da aniyarsa ta sauya sheƙa bayan ta tuntuɓe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ned Nwoko ya zama sanata a inuwar PDP

Kara karanta wannan

Bayan sukar APC, El Rufai ya yi magana kan shirinsa na barin jam'iyyar

An zabi Sanata Ned Nwoko ne a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023.

Idan har ya sauya sheƙa, hakan na nufin cewa dukkan sanatoci uku da ke wakiltar jihar Delta a majalisar dattawa, za su kasance a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Sanatocin Delta ta Tsakiya da Delta ta Kudu na jam'iyyar APC ne bayan sun samu nasara a zaɓen 2023.

Ned Nwoko, wanda shahararren ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa, yana ɗaya daga cikin ƴan siyasar ke da matuƙar tasiri a yankin Delta ta Arewa.

Sai dai, babu kyakkyawar fahimtar juna tsakaninsa da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da kuma tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa.

Sanata Nwoko ba ya shiri da gwamnan Delta

Rashin jituwar da ke tsakaninsu ta samo asali ne kan zargin wariyar da ake yi wa Sanata Nwoko a mazaɓarsa, inda ake ganin Gwamna Oborevwori ya fi karkata wajen biyan buƙatun tsohon gwamna Okowa, wanda shi ne ubangidansa a siyasance.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

Sanata Nwoko da tsohon gwamna Okowa sun fito ne daga yankin Delta ta Arewa.

Alamu sun nuna cewa Okowa, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 amma ya sha kaye, yana harin kujerar sanatan mai wakiltar Delta ta Arewa a zaɓen 2027.

Sauya shekar Nwoko zuwa APC zai zama wani babban ci gaba a siyasar jihar Delta, musamman ganin cewa hakan zai ƙara ƙarfafa jam’iyyar APC a yankin.

Sai dai, hakan kuma babban koma baya ne ga jam’iyyar PDP da ke fuskantar matsaloli daban-daban a siyasarta a yankin.

Ɗan takarar NNPP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Oyo a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Popoola Olukoyade Joshua ya sauya sheƙa zuwa APC.

Popoola wanda ya yi takarar gwamnan a zaɓen 2023, ya koma APC ne domin haɗa kai da shugabannin jam'iyyar wajen ganin sun ƙwace mulki a hannun PDP.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya samu tarba daga wajen shugaban APC na jihar Oyo da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng