Sanatan APC Mai Takaddama da Gwamna Ya Yi Magana kan Ficewa daga Jam'iyyar

Sanatan APC Mai Takaddama da Gwamna Ya Yi Magana kan Ficewa daga Jam'iyyar

  • An yi ta yaɗa jita-jita kan cewa sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha na shirin sauya sheƙa daga jam'iyyar APC
  • Sanatan da ake rikice da shi ya fito ya musanta waɗannan rahotannin inda ya bayyana su a matsayin marasa tushe balle makama
  • Ya buƙaci jama'a da su yi watsi da waɗannan rahotannin domin har yanzu yana nan daram a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha, ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana shirin barin jam'iyyar APC.

Sanata Saliu Mustapha ya bayyana cewa yana nan daram-dam a matsayin mamba na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Saliu Mustapha ya musanta barin APC
Sanata Saliu Mustapha ya musanta ficewa daga APC Hoto: Senator Saliu Mustapha
Asali: Original

Sanata Saliu Mustapha ya musanta jita-jitar barin APC

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Nasif Solagberu, ya fitar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Saliu Mustapha ya kuma musanta rahotannin da ke cewa ya fice daga APC, yana mai bayyana cewa wannan jita-jitar ba ta da tushe balle makama.

Saliu Mustapha ya tabbatar da cewa ya ƙudiri niyyar ci gaba da wakilci nagari ga al’ummar mazabar Kwara ta Tsakiya, rahoton Tribune ya tabbatar.

Sanatan dai yana taƙun saƙa da gwamnan jihar Kwara, Abdurahman Abdulrazaq.

Me Sanatan ya ce kan ficewa daga APC?

"Mun samu labarin wasu rahotannin ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta, masu iƙirarin cewa Sanata Saliu Mustapha, Turakin masarautar Ilorin, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC."
“A magana ta gaskiya bisa tsarinmu, ba mu tsayawa maida martani kan labaran ƙarya. Wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka zaɓi yin shiru cikin ƴan makonnin da suka gabata, duk da jita-jitar ƙarya da wasu ke yaɗawa a kafafen sada zumunta."
"Sanata Saliu Mustapha yana nan daram kan aikinsa na wakiltar al’ummar mazabar Kwara ta Tsakiya a majalisa. Ya maida hankali kan sauke wannan nauyin, kuma ba zai bari jita-jita marasa tushe ta kawar masa da hankali ba."

Kara karanta wannan

Bayan sukar APC, El Rufai ya yi magana kan shirinsa na barin jam'iyyar

"Don fayyace gaskiya, yana da muhimmanci a sani cewa har yanzu Sanata Saliu Mustapha mamba ne mai kishin APC, kuma yana yin cikakkiyar biyayya ga jam’iyyar."
"A matsayinsa na ɗaya daga cikin mutanen da suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tarihi ta Fabrairu 2013 wacce ta haɗa jam’iyyu uku don kafa APC, gudunmawar da ya bayar wajen kafawa da gina jam'iyyar ba ɓoyayya ba ce."

- Nasif Solagberu

Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar, inda ta ce masu yaɗa ta ba su aikin yi ne kawai.

Ɗan takarar gwamna ya koma jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamnan Oyo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP, Popoola Olukayode Joshua ya sauya sheƙa zuwa APC.

Popoola Olukayode Joshua ya bayyana cewa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC ne domin haɗa kai da shugabanninta wajen ƙwace mulki a hannun PDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng