Kogi: Jimami Yayin da Shahararren Dan Siyasar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Awanni Kadan Kafin Zabe

Kogi: Jimami Yayin da Shahararren Dan Siyasar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Awanni Kadan Kafin Zabe

  • Ana saura kwana daya zaben gwamna a jihar Kogi, wani babban dan siyasa ya mutu a safiyar yau Juma’a
  • Marigayin, Muhammad Danasabe Muhammed shi ne shugaban karamar hukumar Lokoja babban birnin jihar
  • Rahotanni sun tabatar cewa marigayin ya fadi a gidansa a daren jiya Alhamis kafin ya ce ga garinku a safiyar yau Juma’a

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Shugaban karamar hukumar Lokoja Honarabul Muhammad Danasabe Mohammed ya riga mu gidan gaskiya.

Wannan na zuwa ne kwana daya tak ya rage a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi a gobe Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Dan siyasa ya riga mu gidan gaskiya ana saura awanni kadan zaben gwamna a Kogi
Marigayin ya rasu a yau Juma'a a Lokoja. Hoto: Comr Abubakar Muhammad.
Asali: Facebook

Yaushe dan siyasar ya mutu a Kogi?

An tabbatar da cewa marigayin ya mutu ne da misalin karfe 4:30 na asuba a asibitin Lokoja babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Zan gina mu ku otal a kan ruwa, dan takarar gwamna a jihar Kogi ya yi alkawari, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa an dauki Muhammad zuwa asibiti bayan ya fadi a gidansa da ke birnin.

An tabbatar da cewa marigayin a cikin ‘yan kwanakin nan ya kasance kullum a cikin ganawar siyasa yayin da ake shirye-shiryen zabe a jihar.

Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar cewa an dauki marigayin zuwa asibitin Shifa bayan faduwarshi a daren Alhamis 9 ga watan Nuwamba.

Mene martanin jam'iyyar APC a Kogi?

Majiyar ta ce:

"Likitoci sun tabbatar da mutuwar marigayin da misalin karfe 4:30 na asubar Juma'a."

Kakakin jam'iyyar APC a jihar, Talba Lakwaja ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma'a 10 ga watan Nuwamba, Legit ta tattaro.

Lakwaja ya ce za a binne marigayin da misalin karfe 2 na rana bayan sallar Juma'a a makabartar Unguwar Kura da ke Lokoja a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Fubara ya gana da Wike, Ya ce ‘mai gida na har gobe’

Kungiya ta nemi a kama Melaye

A wani labarin, Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta bukaci a kama Dino Melaye kan zargin ta'addanci a jihar yayin zabe.

Kungiyar na zargin Melaye da aiwatar da ta'addanci a shekarar 2007 yayin zaben Majalisar Tarayya a jihar.

Kungiyar ta ce Dino ya jagoranci ta'addanci wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dama a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel