Fitaccen Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi Ya Janye Ana Dab da Zabe? Gaskiya Ta Bayyana

Fitaccen Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi Ya Janye Ana Dab da Zabe? Gaskiya Ta Bayyana

  • Jam'iyyar SDP ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa dan takararta a zaben gwamnan Kogi, Muritala Yakubu Ajaka ya janye daga daga tseren
  • Daraktan labarai na kungiyar yakin neman zaben Muri Abenemi, David Ijele ya bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege
  • Ijele ya ce Ajaka ne zabin mutane don haka ba zai janyewa kowa ba a zaben na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Jam'iyyar SDP ta karyata rade-radin cewa dan takararta a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, Muritala Yakubu Ajaka, ya janye daga tseren.

Kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto jam'iyyar ta bayyana wannan rahoton a matsayin kanzon kurege, cewa wani abu mai kama da haka bai faru ba.

Kara karanta wannan

“Ni matar aure ce”: Ododo, dan takarar APC a Kogi ya yi barambarama yayin da yake shagube ga Dino

SDP ta ce dan takararta na Kogi bai janye ba
Fitaccen Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi Ya Janye Ana Dab da Zaɓe? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Murtala Ajaka
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Lokoja, a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, daraktan labarai na kungiyar yakin neman zaben Muri Abenemi, David Ijele ya bukaci jama'a da su yi watsi da wannan rahoton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Labaran karya na cewa Alhaji Murtala Yakubu Ajaka, dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ya janye daga tseren ko ya yi maja da wata jam'iyya kanzon kurege ne kuma ba shi da tushe balle makama, wannan labarin karya da farfaganda aikin makirai ne, guggun mutane da ke yi wa kansu karya don samun kwanciyar hankali sabanin zahirin gaskiya."

"Ajaka ne zabin mutane" - Jam'iyyar SDP

Ya bayyana Ajaka a matsayin dan takarar da mutane ke so kuma cewa ba zai janyewa kowa ba a matakin da aka kai, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo: Malamin addini ya yi hasashen wanda zai lashe zabe

Ya kara da cewar:

"Muna kira ga jama'a, musamman magoya bayanmu da su yi watsi da wannan wasikar bogi na janyewa daga tsere wanda ke yawo a intanet. Ba Isaiah Davies Ijele da Ocheja Unekwu bane suka sanya hannu a wasikar. Wannan wasikar bogin ita ce mataki na karshe da ya ragewa gwamnati mai barin gado da hadimansu."

Gwamnan Kogi: Yan takara 18 zasu fafata

A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tantance jimillar yan takara 18 domin fafatawa a zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.

Yan takarar suna fafutuka don karbar mulki daga hannun Gwamna Yahaya Bello mai ci a watan Janairun 2024.

Manyan yan takara a zaben sune, Usman Ahmed Ododo na jam'iyyar APC, Yakubu Muritala na jam'iyyar SDP da Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel