Zaben Kogi: Kungiya Ta Nemi a Kama Dino Melaye Kan Dalili 1 Tak, Ta Yi Bayani

Zaben Kogi: Kungiya Ta Nemi a Kama Dino Melaye Kan Dalili 1 Tak, Ta Yi Bayani

  • Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta yi kira ga jami’an tsaro da su cafke dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Kogi
  • Kungiyar na zargin Melaye da aikata ta’addanci yayin zaben Majalisar Tarayya da aka gudanar a 2007
  • Ta kuma bukaci sifetan ‘yan sanda, Kayode Egbetokun da ya yi gaggawar kame wadanda su ke da hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Gamayyar Kungiyoyin Kare Muradun Al’umma ta bukaci a kama dan takarar gwamna a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne kan zargin ta’asar da Melaye na jam’iyyar PDP ya aikata a shekakar 2007, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan makomar zaben sabon sanatan APC

Kungiya ta bukaci kama Dino Melaye kan zargin ta'addanci
Kungiya ta bukaci jami'an tsaro su kama Dino Melaye. Hoto: CCSG.
Asali: UGC

Mene kungiyar ke cewa kan Dino Melaye?

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a makon da ya gabata, shugabanta, Wisdom Chinedu ya bukaci sifetan ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya kamo Melaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar na zargin Melaye da PDP da zargin ta’addanci kan abokan hamayyarsa a zaben da ya yi nasara a mazabar Kabba/Bunu/Ijumu a shekakar 2007.

Daga cikin wadanda su ka rasa ransu akwai Mista Jimoh Asimi da Honarabul Victor Obafaiye yayin rikicin, cewar Leadership.

Mene ya faru a Kogi a 2007?

Mista Asimi shi ne wakilin jam’iyyar ACN kafin ta hade da sauran jam’iyyu su dawo APC, sai kuma Obafaiye shi ne shaida a shari’ar zaben da aka gurfanar da Melaye.

Dan takarar jam’iyyar a zaben, Honarabul Richard Akanmode ya gurfanar da Melaye a gaban kotun zaben kan magudi da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar tsohon gwamnan Gombe

Sanarwar ta ce:

“Yayin da ake shari’ar zaben, Honarabul Akanmode ya na da wani shaida wanda a idonsa komai ya faru inda mutane da dama su ka tsira da kyar.
“Abin takaici, ana saura kwana daya a koma kotu, Obafaiye ya samu kirar waya a daren ranar Lahadi inda aka umartce shi da ya fito waje.
“Wannan ita ce ranar ta karshe da sake jin duriyar Obafaiye inda aka fasa masa kayi a wannan ranar.”

Fasto ya yi hasashen zaben Kogi

A wani labarin, wani Fasto ya yi hasashen wanda zai yi nasara a zaben jihar Kogi a watan Nuwamba.

Fasto Godwin Ikuru shi ya bayyana haka inda ya ce Usman Ododo na jam'iyyar PAC shi zai lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel