Zan Gina Mu Ku Otal a Kan Ruwa, Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi Ya Yi Alkawari, Ya Fadi Dalili

Zan Gina Mu Ku Otal a Kan Ruwa, Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi Ya Yi Alkawari, Ya Fadi Dalili

  • Sanata Dino Melaye, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi ya yi albishir ga ‘yan jihar a ayyukan ci gaba
  • Melaye ya yi alkawarin gina otal na alfarma a kan ruwa don jawo ma su zuba hannun jari da yawon bude ido a jihar
  • Dino ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 9 ga watan Nuwamba yayin kamfe na neman kuri’un jama’a a jihar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Dan takarar gwamnan jihar Kogi a jam'iyyar PDP, Dino Melaye ya yi alkawarin mayar da jihar wurin yawon bude ido.

Melaye ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 9 ga watan Nuwamba yayin kamfe din zaben gwamnan da ake shirin yi a gobe Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Kogi: Dino Melaye ya lissafa jerin sunayen yan siyasa da ske son kashewa

Dino Melaye ya yi alkawarin gina otal na alfarma a kan ruwa idan ya samu nasara
'Yan siyasa na ci gaba da alkawura ga al'umma a jihar Kogi. Hoto: Dino Melaye.
Asali: Instagram

Mene Melaye ke cewa a Kogi?

Dan takarar musamman ya yi alkwarin gina otal na alfarma a kan ruwa don jawo ma su hannayen jari daga kasashen ketare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da neman kuri’un mutanen jihar Kogi a zaben da za a gudanar a gobe, cewar Premium Times.

Ya ce:

“Za mu mayar da jihar Kogi wurin yawon bude ido ga kasashen ketare, za mu inganta harkokin yawon bude ido a kan ruwa.
“Za mu gayyato dukkan ma su ruwa da tsaki a harkar yawon bude ido a kasashen duniya don samar da abubuwan more rayuwa.
“Za mu gina otal na alfarma a kan ruwa wanda hakan zai jawo ma su zuba hannun jari da yawon bude ido daga kasashen ketare.”

Wane alkawari Melaye ya yi a Kogi?

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

Meleye ya kuma yi alkawarin gina manyan makarantu da za su yi gogayya da manyan makarantun duniya a jihar, HT Syndication ta tattaro.

Ya kara da cewa:

“Idan mu ka samu nasarar cin zabe za mu gina manyan makarantu, za mu yi tunani sosai wurin inganta harkar ilimi da kawo gyara a tsarin karatu.”

Hausa Legit ta ji ta bakin wasu kan wannan lamari:

Sani Adamu ya ce:

"Matsalar 'yan PDP kenan ba su san yadda za su yi kamfe ba, shiyasa su ke shan kaye a zabe.

Abubakar Yusuf ya ce ai duk wannan yaudara ce dukkan 'yan siyarar haka su ke kawai idan zabe ya zo.

Aisha M. Hussaini ta ce duk ba maganar alkawuran zabe ba ne, Allah ya sa a gama lafiya.

Zaben Kogi: Kungiya ta bukaci a kama Dino

A wani labarin, wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta bukaci a kama Dino Melaye dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi.

Kungiyar na zargin Melaye da ta’addanci a shekarar 2007 yayin zaben Majalisar Tarayya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel