Rikicin Rivers: Fubara Ya Gana da Wike, Ya Ce ‘Mai Gida Na Har Gobe’

Rikicin Rivers: Fubara Ya Gana da Wike, Ya Ce ‘Mai Gida Na Har Gobe’

  • Daga alama dai rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara, da ministan Abuja, Wike, ya zo karshe biyo bayan wata haduwa da gwamnonin suka yi a wajen wani taro
  • A haduwar ta su, Fubara ya ajiye makaman yakinsa, inda ya kira Wike da 'mai gidana' tare da jaddada cewa zai ci gaba da kallonsa a matsayin oga
  • Hakazalika, Fubara ya shaidawa Wike cewa ba shi ne ya ba magoya bayansa umurnin cin mutuncin wani ba, sannan ya bukaci su hada kai don samar da ci gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Rivers - A ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, zai ci gaba da zama shugabansa.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron bikin hukumar shari’a ta jihar Rivers na 'shekarar shari’a' ta 2023-2024, taron da shi ma Wike ya halarta.

An gudanar da taron ne a cocin Anglican na Saint Cyprian, 'Hospital Road', da ke a babban birnin jihar.

Wike, Fubara
Fubara ya gana da Wike, ya ce 'oga na har gobe oga ne', kuma bai sa kowa ya zagi wani ba Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai mun hada kai za a samu ci gaba a Rivers - Fubara

Fubara ya yi nuni da cewa jihar Rivers za ta iya samun ci gaba ne kawai idan akwai zaman lafiya a tsakanin jigogin siyasar da magoya bayansu, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ya ce:

"Ogana zai ci gaba da zama shugabana, duk abin da ya faru a baya, yariga da ya wuce. Ni ban aiki kowa ya zagi wani ba."

Bugu da kari, gwamnan ya yi gargadi ga wadanda suke goyon bayan shi da su guji tozarta abokan hamayyar sa ta hanyar yin kalaman batanci, inda ya bayyana cewa bai ba su izinin yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Bayelsa: Abin da ya sa zan samu nasarar zarcewa - Gwamna Diri ya yi bayani

Ko rikicin Fubara da Wike ya zo karshe?

A cewarsa, a duk sa'ilin da ake kokarin kawo ci gaba, shaidan zai rika kai hari, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne "gano shaidan, da kawar da shi."

Jaridar The Nation ta ruiwato cewa wannan dai shi ne karon farko da ‘yan siyasar biyu wadanda fadan siyasarsu ya mamaye kasar, suka gana da juna a bainar jama’a a jihar.

Abubuwan da Suka Haddasa Rigima Tsakanin Wike, Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai wasu manyan abubuwa guda biyu da suka haddasa rikici a tsakanin Wike da Gwamna Fubara.

Rahotanni sun yi nuni da cewa daga cikin abubuwan da suka haddasa rikici a tsakaninsu har da, nada sabbin kwamishinoni da Fubara ya yi ba tare da sanin Wike ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel